Shugabar NLC Ta Bayyana Wadanda Suka Hana Tinubu Ya Kai Karancin Albashi N100, 000
- Kungiyar NLC ta na ganin ba N70, 000 gwamnatin tarayya ta yi niyyar tsaidawa ya zama mafi karancin albashi ba
- Shugabar NLC a Legas ta yi ikirarin gwamnonin jihohi da su ka dage a kan batun N50, 000 suka yi masu bukulu
- Kwamred Funmi Sessi ta na tunanin gwamnatin Bola Tinubu ta yi niyyar a biya ma’aikaci akalla N10, 000 a wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - An tsaida magana cewa N70, 000 zai zama mafi karancin albashin ma’aikata a wata a Najeriya, hakan ya bar baya da kura.
Mutane sun yi mamaki yadda kungiyoyin kwadagon da su ka kafe a kan akalla N250, 000 su ka dawo su ka yi na’am da albashin N70, 000.
NLC: 'Yan kwadago sun gamsu da N70, 000?
A wani rahoto da Vanguard ta fitar, an fahimci cewa kungiyar NLC ta reshen jihar Legas ta na ganin mafi karancin albashin ya yi kadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan kwadagon sun ce N70, 000 ba za ta rike ma’aikaci a wata ba idan aka yi la’akari da yadda rayuwa ta yi tsada musamman a yanzu.
Kungiyar NLC ta ga laifin gwamnoni
Shugabar NLC a Legas ta zargi gwamnonin jihohi da hannu wajen rashin amince da biyan kudi masu yawa a matsayin mafi karancin albashi.
Kwamred Funmi Sessi ta soki yadda gwamnoni su ka dage ba za su iya biyan ma’aikatan gwamnati abin da ya haura N50, 000 a wata ba.
"Mun san cewa da shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da abin da ya fi N70, 000 amma kungiyar gwamnoni ta fake a kan N50, 000."
"Mun yi imani cewa da shugaban kasa Tinubu ya amince da albashin kusan N100, 000 ne."
- Kungiyar NLC
An rahoto ‘yar kwadagon ta na godiya duk da cewa ba haka aka so ba, amma ta ce hakan ya fi N62, 000 da aka fara kawowa da farko.
Kira ga gwamnatoci kan karin albashi
A jawabin da ta yi, shugabar ‘yan kwadagon ta yi kira ga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi la’akari da kyau da ma’aikata.
Sessi ta na so gwamnotocin Ribas, Legas da Abuja su biya ma’aikatan Legas albashin da zai isa saboda tsadar abinci, sufuri da wurin zama.
An shawo kan NLC kan karin albashi
Labari ya zo cewa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi zai isa gaban majalisa a makon gobe domin shirin aiwatar da shi a fadin Najeriya.
Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu ya yi wa ƴan kwadago alƙawarin shirya kudirin zuwa Talata kuma sun amince da N70,000 a ganawarsu.
Asali: Legit.ng