Majalisa Ta Dauko Hanyar Rage Farashin Siminti, Ta Titsiye Dangote da Sauran Kamfanoni
- Hauhawar farashin siminti a ƙasar nan ya damu majalisar wakilai inda ta fara ɗaukar matakai kan matsalar
- Kwamitin majalisar da ke bincike kan hauhawar farashin ya yi zama da manyan kamfanonin da ke samar da siminti a ƙasar nan
- Shugaban kwamitin ya buƙaci kamfanonin Dangote da Lafarge da su gabatar da dalilan da suka sanya farashin simintin yake ƙaruwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai da ke binciken hauhawar farashin siminti a ƙasar nan, ya fara zama da manyan kamfanonin da ke samar da simintin.
Kwamitin ya buƙaci manyan kamfanonin da su gabatar da takardu kan kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da shi wanda ya sanya farashinsa ya tashi a kasuwa.
Kwamitin ya yanke shawarar ziyartar masana'antun samar da simintin na kamfanonin bayan sun ga takardunsu da nufin gani da ido kan abin da ake kashewa wajen samar da shi domin samar da farashi mai kyau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace buƙata aka nema wajen Dangote da Lafarge?
Shugaban kwamitin, Jonathan Gaza (APC-Nasarawa) ne ya buƙaci hakan a ranar Juma’a a yayin zaman kwamitin inda ya yi tambayoyi kan kamfanonin simintin Dangote da Lafarge Africa Plc a Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.
Ya bayyana cewa kwamitin na son sanin abin ake kashewa wajen samar da siminti tun daga 2020 har zuwa yau wanda ya sanya farashin ya wuce sama da N10,000 a wasu sassan ƙasar nan.
Ya buƙaci kamfanonin su ba da matsakaicin abin da suke amfani da shi na kwal, gas da sauran sinadarai da matsakaicin adadin simintin da suke samarwa a kullum tun daga 2020 har zuwa yau.
Jonathan Gaza ya buƙaci kamfanonin su gabatar da bayanai kan dukkanin abubuwan da aka shigo da su domin samar da siminti da farashinsu tun daga 2020 har zuwa yau.
Ɗan majalisar ya ce ya kamata kamfanonin su kuma ba da cikakkun bayanai kan abubuwan da ake amfani da su a cikin gida domin samar da siminti da farashin su a Naira da Dala.
Jonathan Gaza ya kuma ce kamfanonin su bayar da bayanai kan harajin da aka yafe musu da bayanai kan kwamgilolin gas da sinadaran fashewa.
Ƴan majalisa sun nemi alfarma kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta buƙaci masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan da su haƙura.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Alhamis inda ta buƙaci masu shirya zanga-zangar ɗauki dangana tare da tattaunawa da gwamnati.
Asali: Legit.ng