N70,000: Kalubale 5 da Ke Gaban 'Yan Kwadago da Ma’aikata Bayan Karin Albashi

N70,000: Kalubale 5 da Ke Gaban 'Yan Kwadago da Ma’aikata Bayan Karin Albashi

  • A jiya Alhamis ne kungiyar kwadago da gwamnatin shugaba Bola Tinubu su ka samu daidaito kan maganar ƙarin albashin ma'aikata
  • Kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya sun samu amincewa kan biyan ma'aikata N70,000 a mafi ƙarancin albashi duk wata
  • Sai dai har yanzu akwai kalubalen da ma'aikatan Najeriya da kungiyar kwadago za su fuskanta a Najeriya kan karin albashin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A jiya Alhamis kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya suka samu daidaito kan batun karin albashi.

Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da biyan ma'aikata N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Karin Albashi
Kalubalen da ke gaban yan kwadago da ma'aikata bayan karin albashi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu| Nigerian Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro muku kalubale da ma'aikatan za su fuskanta a yanzu haka da ke murnar karin mafi ƙarancin albashin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: NLC ta yi barazanar tsunduma wani yajin aiki, an gano dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Rashin amincewar wasu ma'aikata

Tun a jiya da aka sanar da karin albashin wasu ma'aikata a jihar Osun suka fara nuna kin amincewa da kudin kan cewa ya yi kadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Masana suna ganin hakan kalubale ne da zai iya shafar hadin kan kungiyoyin kwadago a Najeriya.

2. Ma'aikatu masu zaman kansu

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa ma'aikatu masu zaman kansu sun nuna damuwa kan karin kudin.

Sun bayyana cewa kudin ya yi yawa kuma sun fara gindaya sharudda kafin biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashin N70,000.

Wannan kalubale ne ga kungiyar kwadago da ma'ikata da suke aiki tare da ma'aikatu masu zaman kansu a Najeriya.

3. Matsalar gwamnonin jihohi

Tun da aka fara maganar ƙarin albashi gwamnonin jihohi suka rika nuna cewa ba za su iya biyan kudi mai yawa ba.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi tare da daukar alkawura 3

Gwamnonin sun nuna cewa zai fi dacewa a bar kowace jiha ta biya ma'ikata abin da za ta iya wanda hakan ya fusata yan kwadago har da fara shirin yajin aiki.

Wannan ma kalubale ne babba ga yan kwadago kasancewar gwamnonin jihohi ba lallai su iya fara biyan kuɗin ba.

4. Yaushe za a fara biyan ma'aikata?

Tun da aka samu yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da yan kwadago ake tambayar yaushe za a fara samun karin.

Har yanzu dai ba a samu magana tsayayya daga gwamnati ba duk da cewa shugaba Tinubu ya tura bukatar ƙarin kasafin kudi zuwa majalisa.

5. Albashin N70,000 za ta isa ma'aikaci?

Wani babban kalubale da ma'aikatan za su fuskanta shi ne cewa kudin da aka kara ba zai iya tabuka abin kirki wajen sayayya ba.

Masana sun ce hakan kuma abin lura ne inda kayayyakin masarufi suka ninka kudi a kasuwannin Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin kawo tsarin da zai ba Tinubu damar zarce shekara 4 ba tare da zabe ba

Gwamna Fubara ya karyata jita-jitar albashi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Ribas ta musanta labarin da yake cewa za ta biya sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiha da kananan hukumomi.

Gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu inda gwamnatinsa ta ayyana aniyar biyan N80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng