Fusataccen Malamin Addini Ya Zane Mabiyansa Kan Saba Doka, Sun Sha Mamaki

Fusataccen Malamin Addini Ya Zane Mabiyansa Kan Saba Doka, Sun Sha Mamaki

  • Wani fusataccen Fasto a jihar Enugu ya zane mambobin cocinsa saboda sun ki share harabar wurin ibadar yadda ya umarta
  • Fasto Linus Okwu ya dauki matakin ne a cocinsa da ke karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar inda ya zane har da manya
  • Lamarin ya tayarwa mambobin cocin hankali inda wata ta ce ta koma gida jikinta duk shatin bulali duk da girmanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Fusataccen Fasto a jihar Enugu ya zane mabiyansa saboda kin share harabar cocinsa.

Faston mai suna Linus Okwu ya dauki matakin ne kan mambobin da suka hada da manyan mata da matasa domin kare faruwar hakan a gaba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Malamin addini ya bulale mabiyansa saboda kin bin umarninsa
Fusataccen Fasto a jihar Enugu ya zane mambobinsa kan kin share coci. Hoto: Legit.
Asali: Original

Fasto ya zane mabiyansa a coci

Lamarin ya faru ne a garin Agbani da ke karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fusataccen Faston ya shigo cocin dauke da bulali inda yake tambayar dalilin mabiyan nasa na kin share harabar cocin, cewar Daily Post.

Mabiyan sun ba shi dalilai amma bai gamsu ba inda ya bukace su da su tsuguna tare da zuba musu bulali cikin rashin tausayi.

Daya daga cikin mambobin cocin ta ce ta koma gida da shatin bulali a jikinta inda ta ce ta yi mamaki matuka.

Ta ce Faston cikin fushi ya ce musu tun da sun ki bin umarnin coci to zai yi amfani da wani mataki mai tsauri kansu.

Enugu: Martanin mamban cocin kan lamarin

"Faston lokacin da ya ke jawabi gare mu ya nuna bacin ransa saboda mun ki bin umarnin coci."

Kara karanta wannan

Ndume: Daurawa ya nuna fargaba kan gwamnatin Tinubu, ya fadi illar haka gare su

"Ina zaune a sahun gaba tare da wasu matasa lokacin da Faston ya fara zane jama'a ni kuma sai na koma baya saboda ina tunanin ba zai doki manya ba."
"Amma abin mamaki ya zane kowa a cocin har da ni da sauran manyan mutane da ke cikin wurin bautar."

- Cewar mambar cocin

Matar ta ce lokacin da ta yi korafi kan matakin sai ya ce kamar yadda mahaifinta zai zana ta haka shima kamar mahaifinta yake.

Karin albashi: Fasto ya shawarci 'yan Majalisa

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen Fasto a Najeriya, Ejike Mbaka ya yi tsokaci kan mafi karancin albashi a kasar da ake tababa.

Mbaka ya bukaci mayar da mambobin Majalisar Tarayya kan tsarin mafi karancin albashin N62,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi tayi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.