Shiga Jami'a: Duk da Dage Kayyade Shekarun Dalibai, Tsohon Sanata ya Taso Gwamnati a Gaba
Tsohon Sanata a Kaduna, Shehu Sani ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakin kayyade shekarun shiga jami'a ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Shehu Sani ya bayyana cewa Alah (SWT) ya halicci wasu da hazaka, saboda haka hana su shiga jami'a da wuri cutar wa ce gare su
- Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ta ce 'yan shekaru 18 ne kawai za su nemi shiga jami'a, amma an sassauta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ga rashin dacewar matakin da gwamnati ta dauka a kan daliban masu kananan shekaru.
Sanata Shehu Sani ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta haramta wa yan kasa da shekaru 18 samun gurbin karatu a manyan makarantu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Shehu Sani na ganin bai kamata a yi kokarin dakile yara masu hazaka ta hanyar hana su shiga makaranta da wuri ba, ya wallafa a shafinsa na X.
"An haifi wasu da fikira," Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya shiga jerin 'yan Najeriya da su ka caccaki matakin kayyade shekarun daliban da za su shiga manyan makarantu.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa duk da gwamnatin ta soke shirin inda ta mayar da shi shekara 16, amma za a dawo da shi a shekarar 2025.
Amma Sanata Sani ya ce akwai mutanen da Allah ya halicce su da fikira, kuma bai kamata a dankwafar da su ba.
"Ba nutsuwa tattare da yara," Masanin Ilimi
Wasu daga masana ilimi na ganin kayyade shekarun shiga makarantun gaba da sakandare zuwa 18 abu ne mai kyau, saboda 'yan kasa da shekaru 18 ba su da nutsuwar karatu.
Darakta kula da ingancin karatu a kwalejin ilimi ta Kano (FCE), Dakta Ibrahim Adamju Kabuga ya shaidawa Legit cewa da yawa daga daliban da su ke koyar wa 'yan kasa da 18 ba sa fahimta.
Gwamnati ta kayyade shekarun dalibai
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kayyade shekarun dalibai masu sha'awar shiga manyan makarantu zuwa 18, lamarin bai yiwa wasu dadi ba.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana umarnin ga hukumar JAMB, amma an dage tsarin zuwa shekarar 2025, inda daga nan za a daina daukar 'yan kasa da 18.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng