'Yan Bindiga Sun Bindige Shugaban Miyetti Allah, Kungiyar Makiyaya Tayi Kira ga Mutanenta

'Yan Bindiga Sun Bindige Shugaban Miyetti Allah, Kungiyar Makiyaya Tayi Kira ga Mutanenta

  • An shiga jimami bayan ƴan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau
  • Ana zargin yan bindiga sun hallaka matashin mai suna Yakubu Muhammad a daren jiya Alhamis 28 ga watan Yulin 2024
  • Shugaban kungiyar a karamar hukumar Bassa, Ya'u Idris shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 19 ga watan Yulin 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau -'Yan bindiga sun hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah a jihar Plateau.

Marigayin mai suna Yakubu Muhammad ya rasa ransa ne a karamar hukumar Bassa da ke jihar.

An hallaka shugaban matasa na kungiyar Miyetti Allah
'Yan bindiga sun yi ajalin shugaban matasa ƙungiyar Miyetti Allah. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

An hallaka shugaban Miyetti Allah a Plateau

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 18 ga watan Yulin 2024 da misalin karfe 7:40 na dare a yankin Jebu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jigon APC ya yi martani bayan cin mutuncin Dan Bilki Kwamanda, ya ba da shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar a karamar hukumar, Ya'u Idris shi ya tabbatar da kisan matashin inda ya ce abin takaici ne.

Idris ya ce su na zargin an kashe matashin da nufi inda ya bukaci al'umma su kwantar da hankulansu, cewar Tori News.

"Mu mutane ne masu son zaman lafiya da bin doka, mun riga mun kai rahoton ga jami'an tsaro."
"Muna kira ga mutanenmu da su kwantar da hankalansu kan abin da ya faru."

- Ya'u Idris

Miyetti Allah: Kwamandan sojoji ya yi magana

Kwamandan rundunar 'Operation Save Haven' Birgediya-janar, M O Ago ya jajantawa iyalan marigayin inda ya ce an yi rashin jajirtacce matashi.

Kafin rasuwarsa, marigayin na daga cikin kwamitin zaman lafiya da rundunar ta kafa domin dakile hare-hare.

An tsinci gawar soja a Plateau

Kun ji cewa an tsinci gawa wani sojan Najeriya da ya yi ritaya, mai suna Kanal BT Vandi, a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Rahotanni sun tabbatar cewa sojan mai ritaya ya rasu ne a ɗakinsa bayan ya shiga ciki da wasu ƴan sa'o'i kaɗan.

Marigayin Vandi ya shiga ɗakin baƙi na sansanin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, kuma an gano cewa ya mutu ne a ranar Laraba, 17 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.