An Kassara Ayyukan Miyagu, 'Yan Sanda Sun yi Ram da Masu Aikawa 'Yan Bindiga Bayanai

An Kassara Ayyukan Miyagu, 'Yan Sanda Sun yi Ram da Masu Aikawa 'Yan Bindiga Bayanai

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kara samun nasara a kan masu taimaka wa 'yan ta'adda da bayanan sirri domin kai hare-hare
  • Daga cikin wadanda aka kama akwai yaro mai shekar 13 Umar Hassan da wani mai shekaru 70 Lawai Umaru da karin mutum biyu
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq ya ce bayanan da su ka bayar ya taimaka wajen kai farmaki kauyuka da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarar damke wasu mutane hudu da ke tattara bayanan sirrin jama'a su na mikawa masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke sufeto bisa zargin fashi da satar mota

Wani yaro mai shekaru 13, Umar Hassan na daga cikin mutane hudu da jami'an tsaron su ka cafke bisa zargin taimaka wa miyagun.

Nigeria Police Force
An kama masu mika bayanan sirri ga 'yan ta'adda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa sauran mutanen da 'yan sanda su ka kama sun hada Lawai Umaru, mai shekaru 70 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau Ibrahim Lawai mai shekaru 22 da Abdulganiyu Isah shi ma mai shekaru 22.

"An farmaki kauyuka bayan samun bayanai," Yan Sanda

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana kama wasu mutane hudu da su ka rika bayar da bayanan da su ka jawo hare-hare kan kauyuka da dama.

Solace Base ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq ne ya tabbatar da kamen da su ka yi.

Kakakin rundunar ya ce sun yi nasarar kama mutane hudu bayan sun samu bayanan yadda su ke tattaro bayanai kan jama'a da kauyukan da aka rika kai wa hari.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tirela da karamar mota sun yi karo, an yi asarar rayuka

An gano masu mika bayanai ga miyagu

A wani labarin kuma shugaban jami'ar tarayya ta Dustin-ma (FUDMA), Farfesa Armaya'u Bichi ya ce an gano masu mika bayanan ma'aikatan jami'ar ga miyagu.

Farfesa Armaya'u ya ce daga cikin ma'aikatan FUDMA ne aka samu gurbatattu masu mika bayanan, kuma tuni aka tura na su bayanan ga rundunar 'yan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.