Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Sheikh Gumi Ya Karfafi Guiwar Matasa, Ya Soki Malamai

Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Sheikh Gumi Ya Karfafi Guiwar Matasa, Ya Soki Malamai

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce Allah ya aiko matasa domin su dawo da 'yan siyasa cikin hankalinsu
  • Sheikh Gumi ya kuma soki malaman addini da ke nuna cewa zanga-zanga haramun ce alhalin su ba za su fadawa gwamnati gaskiya ba
  • Malamin addinin ya ce ma damar aka ci gaba da tafiya a haka, to babu wanda zai yi saura a kasar nan zuwa nan da shekara hudu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana matukar damuwarsa game da halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Sheikh Gumi ya soki malaman da ke cewa zanga-zanga haramun ce, inda ya ce, “babu malamai, kungiyoyi, ko masu kudi da ke iya yin magana kan matsalolin da ke damun kasar."

Kara karanta wannan

"Tinubu na kokari, kar ku shiga zanga zanga," Minista ya lallabi jama'a

Sheikh Gumi ya soki malaman da ke nuna cewa zanga-zangar adawa da Tinubu haramun ce
Sheikh Gumi ya ce Allah ne ya aiko matasa domin su saita hankalin 'yan siyasa. Hoto: AAGummi, Officialasiwajubat
Asali: Twitter

Fitaccen malamin addinin ya bayyana hakan ne a karatunsa na littafin Risala wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi ya soki malamai kan zanga-zanga

Sheikh Gumi ya ce:

"An wayi gari wani babban dan siyasa a Arewa yana cewa kasar nan ta mutu, babu wani malami, kungiya, ko masu kudi da za su iya yin magana, kasa ta koma karazube.
"Ana cikin hakan ne, sai Allah ya ji kukan bayi, ya fitar da wasu yara da za su tada hankalin hukuma domin ta dawo hankalinta.
"Amma maimakon malamai su jawo yaran su nusar da su yadda ya kamata su yi zanga-zangar, sai suka dawo suna amfani da addini wajen nuna cewa zanga-zangar haramun ce."

Sheikh Gumi ya ce Allah ne ya aiko matasa su yi zanga-zanga domin zama silar gyaruwar 'yan siyasar saboda ba za a iya kamasu ko kashe su ba saboda suna da tarin yawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Kabiru Gombe ya yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a Najeriya

Kalli bidiyon a kasa:

"Zanga-zanga daban, bore daban"- Gumi

Malamin addinin ya bayyana cewa tun a zamanin sahabbai ake nuna adawa da gwamnati, amma a wannan zamanin ne malamai ke danne mutane yayin da ake aikata zalunci.

A wani faifan bidiyon na daban, Sheikh Gumi ya ce akwai bambanci tsakanin bore da zanga-zanga, kamar yadda ya ce:

"Duk wani bore wanda ya hada da daukar makami kamar yadda 'yan Boko Haram, ko 'yan bindiga suka yi, haramun ne.
"Amma Sunnah ne idan aka samu ja'irin shugaba, a samu wasu su je su tsaya a gabansa su ce abu kaza da abu kaza ba daidai bane."

Malamin addinin ya ce ma damar aka ci gaba da tafiya a haka, to babu wanda zai yi saura a kasar sakamakon kowa zai koma kwarangwal saboda tsananin yunwa.

Kalli wannan bangaren a kasa:

Sheikh Gumi ya lissafa sharudan zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sheikh Ahmad Gumi ya ce akwai bukatar al'ummar Najeriya su yi taka tsan-tsan yayin da suka shirya gudanar da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Hana zanga zanga: Malamai sun gana da Tinubu, an gano duka abubuwa 3 da aka tattauna

Malamin addinin ya jaddada cewa yin zanga-zangar lumana bai sabawa doka ba ma damar aka yi ta bisa doton dokar, inda ya nemi matasa da su gujewa karya doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.