Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi

Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi

Tsokacin Edita: Dukkan abubuwan da zasu karanta a wannan rubutu ra'ayin marubucin ne ba ra'ayi Legit.ng Hausa ba.

Hukuncin zanga-zanga a Shariah

Daga Dr Ahmad Gumi

"Idan zanga-zanga ce da nufin ibada ce ita kanta watau 'ta-abbudiyah' to, bidi'ah ce domin babu Zanga-zanga cikin ibadun musulunci. Kamar tattaken arbaeen na Shiah, ko maulidai ga masu yin haka.

Idan kuma ita babin mu'amalah ce da siyasah, to dole ayi tafsili. In tanada amfani a mahangar shariah to hukuncin ta yakan fada akan hukunce hukuncen shariah na wajibci, ko mustahabbi ko Halas ko makaruhi ko Haram.

Zanga-zangar da zata kawo sawyin mulki ko bijirema shugabanni Musulmi masu adalci ko marsa adalci, jairai, masu mugunta, haramun ce. (a saurari Karin bayani daga baya)

Zanga-zangar da zata kawo sawyin halin jamaah zuwa inganta rawuwarsu mustahabbi ce.

Zanga-zangar da zata kawo sawyin halin jamaah zuwa inganta addinin su yajibace amma da sharadin rashin haifar da musiba wadda tafi yadda ake kafin ayita.

Zanga-zangar da zata kawo rarrabuwar kan jamaah ko salwantar dukiya ko rayuka haramun ce magana guda.

Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi
Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi Hoto: Dr Ahmed Gumi
Asali: Twitter

To me Saya aka haramta Zanga-zangar juye mulki daga hannun Musulmi ko da jairine?

1. Mulki na Allah ne - Subhanahu Wa Taala, Shi Ya haramta Musulmi suyi jayayya kan mulkinSa.

2. Duk abunda da zai kai ga fada tsakanin Musulmai haramunne.

3. Tashin hankali domin neman mulki Bai haifar da da Mai ido. Duk locakin da mutane suka hada kansu domin su juye mulki sai suma sun hainci kanuwansu. Karshenta a wahala fiye da farko.

Saboda haka, a irin wannan tsari, na demokiradiya, dama yazo cikin kundinshi da halarcin Zanga-zanga ta lumana saboda haka baa iya haramta ta da sunan addini. Sai Dai, idan akwai yuyuwar shigan muyagun mutane da zasu karkatar da ita zuwa wata muguwar manufa ta cutar da addini ko yanayi ko salwantar da dukiya ko rayuka ko cin mutuncin mutane to wannan haramun ne a Shariah.

Wallahu 'Alam.

Allah Ya bamu dacewa, Ya kawo muna taimako daga wurinsa da kuma Zaman lafiya. Kuma Ya hada kanmu akan gaskiya da dukkan alheri. Amin."

KU KARANTA WANNAN: Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng