"Za Mu Hukunta Duk Wanda Ya Karkatar da Tallafin Manoma," Abba Gida Gida Ya Dauki Zafi

"Za Mu Hukunta Duk Wanda Ya Karkatar da Tallafin Manoma," Abba Gida Gida Ya Dauki Zafi

  • Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta saurara wa duk wanda aka kama da kokarin karkatar da tallafin takin zamani da aka raba ga manoma ba
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin raba tallafin takin zamani ga manoma 52,000 daga dukkanin kananan hukumomin jihar
  • A gargadin da ya aika ga jami'an gwamnati, Abba Kabir Yusuf ya ce an raba tallafin ne domin ya isa ga manoma na hakika ba aljihun wasu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi jami'an gwamnatin Kano da su guji karkatar da tallafin takin manoman jihar.

Kara karanta wannan

"Ban ce zan biya N80,000 ba," Gwamna ya musanta rahoton zai yi karin albashi

Gwamnatin Kano ta fara raba tallafin takin zamani ga manoma 52,000 a kananan hukumomin jihar 44 domin bunkasa harkokin noma.

Gwamna
Gwamna Abba Gida Gida ya gargadi masu niyyar karkatar da tallafin takin manoma Hoto: Sanusi Bature
Asali: Facebook

Gargadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da darakta janar ka yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida-Gida ya ja kunnen jami'ansa

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta saurara wa duk jami'in da aka kama ya na karkatar da takin manoma ba.

Daily Trust ta wallafa cewa Abba Kabir Yusuf ya ce za su hukunta duk wanda aka kama da kokarin almundahanar takin.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci rashawa ba, domin an raba tallafin ne domin manoma na hakika.

Sarkin Kano ya nemi a tallafawa manoma

Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya nemi masu hannu da shuni su taimaka wa manoma a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

Ya ce akwai bukatar tallafin ga manoma da sauran talakawan gari, musamman a halin da ake ciki na babu.

Sanusi II ya yaba da yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara bijiro da tsare-tsaren da za su taimaki talakawa.

Abba Gida-Gida ya dauko manyan ayyuka

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauko muhimman ayyuka hadin gwiwa da kananan hukumomi da za su canja rayuwar mazauna Kano.

Wasu daga cikin ayyukan da za a gudanar sun hada da gyaran tituna da gina sababbi, inganta lantarki da biyan bashin albashin masu shara da gudanar da ayyukan mazabu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.