Adawa da Tinubu: Gwamnati Ta Gano Wadanda Ke Daukar Nauyin Matasa Su Yi Zanga Zanga

Adawa da Tinubu: Gwamnati Ta Gano Wadanda Ke Daukar Nauyin Matasa Su Yi Zanga Zanga

  • Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar NOA ta ce ta gano wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar
  • Hukumar NOA ta bayyana cewa masu daukar nauyin zanga-zangar na son tayar da zaune tsaye, kashe-kashe da kuma raunata 'yan kasa
  • Kamar yadda NOA ta bayyana a wata sanarwa, gwamnati ta dauki matakai na ganin ta dakile mugun nufin masu shirya zanga-zangar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) ta ce ta gano wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan.

An ruwaito cewa wasu ‘yan Najeriya na shirin gudanar da zanga-zanga tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agusta domin nuna adawa da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan wanda ya kai hari masallaci ana asuba

Hukumar NOA ta yi magana kan masu daukar nauyin zanga-zanga a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta gano wadanda suka dauki nauyin matasa su gudanar da zanga-zanga. Hoto: @NOA_Nigeria
Asali: Twitter

Paul Odenyi, mataimakin daraktan yada labaran hukumar ne ya sanar da cewa sun gano masu daukar nauyin zanga-zangar a cikin wata sanarwa da NOA ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano masu hannu a shirin zanga-zanga

Sanarwar da aka fitar a ranar Alhamis ta ce hukumar NOA baya ga gano wadanda ke daukar nauyin zanga-zangar, ta kuma gano wuraren da matasan za su rufe.

Odenyi ya ruwaito Lanre Issa-Onilu, Darakta-Janar na hukumar yana cewa masu daukar nauyin zanga-zangar suna da niyyar "bata sunan Najeriya a idon kasashen duniya."

Issa-Onilu ya bukaci masu zuga matasa su fita zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar da su rungumi "zama a teburin tattaunawa" a maimakon yin zanga-zanga.

“Mun gano bayanan da yawa daga cikin wadanda suka dauki nauyin gudanar da wannan zanga-zangar, tare da masu hure masu kunne da ke zaune a kasashen waje."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: NLC ta yi barazanar tsunduma wani yajin aiki, an gano dalili

- Paul Odenyi.

An bankado shirin masu shirya zanga-zanga

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Ba wai gwamnati ko halin da kasar ke ciki ne makasudin shirya zanga-zangar ba, illa dai yaudara ce kawai ta masu daukar nauyin domin tada zaune tsaye a kasar.
"Munufar masu daukar nauyin zanga-zangar ba zai wuce dagula al'amuran kasa, ta da tarzoma, kone-kone, kashe-kashe, da raunata 'yan kasa kawai saboda wata manufa ta siyasa."

Hukumar ta NOA ta ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai domin dakile mugun nufin masu daukar nauyin zanga-zangar, inda ta nemi taimako daga shugabannin al'umma, iyaye, da matasa.

Zanga-zanga: Malamai sun gana da Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dakta Aliyu Muhammad Sani, wani malamin addinin Musulunci ya ce malamai sun gana da Shugaba Bola Tinubu kan halin da kasar ke ciki.

Dakta Aliyu ya ce sun tattauna da Tinubu kan tsaro, samar da abinci, yarjejeniyar Samoa, matsin tattalin arziki da sauransu, sabanin zargin 'yan Najeriya cewa sun karbi na-goro daga gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.