Jami’o’in Arewa 3 Sun Kafa Tarihi a Karon Farko, Sun Samu Kyautar Miliyoyin Kudi
- Hukumar jarrabawar JAMB ta kaddamar da taron karrama jami'o'i da suka yi zarrra a Najeriya kan daukar dalibai ta hanyar da ta dace
- A wannan karon, jami'o'i uku daga Arewacin Najeriya ne suka lashe dukkan kyaututtuka da lambar yabo da hukumar JAMB ta bayar
- Haka zalika hukumar JAMB ta gwangwace dukkan makarantun da kyautar miliyoyin kudi bisa namijin kokarin da suka nuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta karrama jami'o'i da suka fi nuna hazaka a bana.
Jami'o'i uku daga Arewacin Najeriya sun zama sun doke dukkan jami'o'i a fadin Najeriya a wannan karon.
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin sakon da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook kasancewar shi ne bako na musamman a wajen taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
JAMB: Jami'o'i Arewa da suka yi fice
1. Jami'ar Ilorin (Kwara)
Jami'a da ta zama ta farko a bana a bisa tantancewar JAMB a shekarar 2024 ita ce jami'ar jihar Ilorin.
A bisa wannan kokari da ta nuna, hukumar JAMB ta ba jami'ar Ilorin kyautar kudi har Naira miliyan 500.
2. Jami'ar Ahmadu Bello (Zariya)
Jami'ar Ahmadu Bello da ke jihar Kaduna ita ce ke bin jami'ar Ilorin a matsayin ta biyu a wannar shekarar.
Haka zalika hukumar JAMB ta ba jami'ar Ahmadu Bello kyautar zunzurutun kudi Naira miliyan 75 bisa kokarin da ta nuna.
3. Jami'ar jihar Borno
Jami'ar jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya ce ta zamo ta uku a kididdigar JAMB ta bana.
Kuma hukumar JAMB ta gwangwace jami'ar Borno da kyautar kudi Naira miliyan 25 bisa hoɓɓasar da ta yi a bana.
Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna ta zama lamba ta daya a ɓangaren irin nasu haka nan ma kwalejin ilimi ta Zariya da zama ta daya a ɓangaren kwalejojin ilimi a Najeriya.
2024: JAMB ta fadi dalibai masu kokari
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar JAMB ya bayyana sunayen ɗaliban da suka ci maki mafi yawa a jarabawar share fagen shiga jami'a ta bana 2024.
Shugaban JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da sunayen ɗaliban a wurin taron majalisar gudanarwa ta hukumar a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng