Mafi Karancin Albashi: 'Yan Kwadago Sun Bayyana Dalilin Amincewa da N70,000
- Ƙungiyoyin ƙwadago sun amince da tayin shugaban ƙasa Bola Tinubu na N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
- Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa sun amince da tayin ne saboda abubuwa masu gwaɓi da ke cikin yarjejeniyar
- Samun matsaya kan mafi ƙarancin albashin dai ya kawo ƙarshen dogon lokacin da aka kwashe ana tattaunawa tsakanin gwamnati da ƴan ƙwadago kan abin da za a biya ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago sun tabbatar da amincewa Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin da za a riƙa ba ma’aikatan Najeriya.
Shugaban ƙasan ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ne bayan ya kammala tattaunawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ƴan ƙwadago suka amince da N70,000?
Jaridar Daily Trust ta ce da yake zantawa da manema labarai bayan kammala tattauna da shugaban ƙasan, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) Joe Ajaero, ya bayyana cewa sun amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin.
Joe Ajaero wanda yake tare da shugaban ƙungiyar TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa sun amince da tayin ne saboda abubuwa masu gwaɓi da aka sanya a cikin yarjeniyar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Shugaban na NLC ya kuma bayyana cewa wani dalilin da ya sanya suka amince da tayin shi ne alƙawarin da Shugaba Tinubu ya yi na sake waiwayar dokar mafi ƙarancin albashi ta ƙasa duk bayan shekara uku.
Tinubu ya nemi alfarma wajen ƴan ƙwadago
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bukaci kungiyoyin kwadago da su amince da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya, jihohi da kamfanoni suka amince da shi.
Shugaba Tinubu ya tabbatarwa da shugabannin ƙungiyoyin cewa za a riƙa canja mafi ƙarancin albashin duk bayan shekara biyu, uku ko huɗu ba sai ya kai shekara biyar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng