Magana Ta Kare: Tinubu Ya Fadi Sabon Mafi Karancin Albashi Tare da Daukar Alkawura 3
- Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 matsayin sabon mafi karancin albashi
- Hakan na zuwa ne bayan da shugabannin kungiyoyin 'yan kwadago na Najeriya suka gana da shugaban a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Hakazalika, shugaban kasar ya dauki alkawarin waiwayar dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ayyana N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya.
Hakazalika, shugaban kasar ya dauki alkawarin waiwayar dokar mafi karancin albashi na kasa duk bayan shekaru uku.
Tinubu ya yi wa 'yan kwadago albishir
Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan watsa labarai ga Shugaba Tinubu ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni da kananan hukumomi wajen biyan mafi karancin albashin.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a taron da ya yi da shugabannin TUC da NLC ranar Alhamis a Abuja, wanda shi ne karo na biyu da bangarorin suka gana cikin kwanaki 7.
Tinubu ya waiwayi albashin ma'aikatan jami'io'i
Mista Onanuga ya ci gaba da cewa, shugabannin kwadago sun yaba da dattakon Shugaba Tinubu, yana mai cewa:
“Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi tare da yin alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashin duk bayan shekaru uku.
“Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu da na kananan hukumomi wajen biyan mafi karancin albashin"
"Sannan kuma shugaban kasar ya sha alwashin yin amfani da karfin ikonsa na magance rashin albashin watanni hudu da kungiyoyin jami’o’i.
JAMB ta kayyade makin shiga jami'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zana jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta sanar da sabon mafi ƙarancin makin shiga jami'o'i a fadain Najeriya.
Yayin da JAMB ta ayyana maki 140 matsayin mafi karancin makin shiga jami'o'i, hukumar ta ce dalibai za su nemi maki 100 domin shiga kwalejojin ilimi, kimiyya da na fasaha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng