Zargin Harkar Kwaya: Kotu ta yi Hukunci kan Tuhumar Dakataccen Dan Sanda Abba Kyari
- Kotun daukaka kara mai zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta dauki mataki a kan shari'ar dakataccen dan sanda, DCP Abba Kyari
- Kotun ta ki amince wa da dakatar da karar da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta shigar gabanta
- Ama zargin tsohon shugaban rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami da miyagun laifuka da safarar kwaya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta ki amincewa da bukatar dakatar shari'ar da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta shigar kan harkallar kwaya.
A zaman kotun na Alhamis din nan, an bayyana cewa bukatar dakatar da shari'ar da ake yi na tuhumar Abba Kyari da laifukan da su ka shafi safarar kwaya guda takwas bai zai yiwu ba.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa ana zargin Abba Kyari, wanda shi ne tsohon shugaban rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami da miyagun laifukan safarar kwaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne zargi ake yi wa Abba Kyari?
Hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi ta NDLEA ta na tuhumar Abba Kyari da wasu mutum biyu - Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne da safarar kwaya.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa sauran wadanda ake tuhuma tare da Kyari sun hada da CP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Sufeto Simon Agirigba da Sufeto John Nuhu.
NDLEA na zargin Kyari da sauran jama'arsa da almundahanar hodar iblis mai nauyin kilo 21.25 da su ka kwace daga hannun masu safarar kwaya da cinikin hodar mai nauyin kilo 17.55.
Dukkanin wadanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da hukumar NDLEA din ke yi masu.
Abba Kyari ya bayyana gaban kotu
A baya mun kawo labarin cewa hukumar yaki da hana fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta sake mika DCP Abba Kyari a gaban kotu bisa zargin harkallar kwayoyi.
An dawo da dakataccen jami'in dan sandan a gaban kotu da sauran mutane shida ne bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, amma Abba Kyari ya ki amsa tuhumar da ake yi masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng