Uba Sani Ya Ba da Umarnin a Zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna Ta Magantu

Uba Sani Ya Ba da Umarnin a Zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna Ta Magantu

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya nisanta kansa da bidiyon dukan Ɗan Bilki Kwamanda da ke yawo a intanet
  • Kamar yadda gwamnan ya sanar a takardar da ya fitar, yace ba ya cin zarafin mutum kawai don su na da bambancin ra'ayi a siyasa
  • Gwamnatin Kaduna za ta bincika tare da gano tushen lamarin tare da tabbatar da masu dukan sun fuskanci fushin hukuma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta nesanta kanta daga bidiyon da ya bazu a shafukan sada zamunta wanda aka ga wasu mutane suna zane Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda.

Wani bidiyo da ya yadu ya nuna yadda aka zane Ɗan Bilki Kwamanda sannan ake tuhumarsa da zagin gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, lamarin da ya janyo cece kuce.

Kara karanta wannan

'Yan Kannywood sun fusata da ganin bidiyon da ake lakadawa Dan Bilki Kwamanda duka

Gwamnatin Kaduna ta yi magana kan dukan da aka yiwa Dan Bilki Kwamanda
Gwamnatin Kaduna ta nesanta kanta daga dukan da aka yiwa Dan Bilki Kwamanda. Hoto: @kokikano3, @ubasanius
Asali: Twitter

Abdallah Yunus Abdallah, babban mataimaki na musamman (shafukan sada zumunta) ga gwamnan Kaduna ne ya fitar da sanarwar hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya magantu kan dukan Dan Bilki

Sanarwar mai dauke da sa hannun Muhammad Lawal Shehu, babban sakataren watsa labarai na gwamnatin Kaduna, ta ce abin da aka yi wa Dan Bilki Kwamanda ya tauye hakkinsa.

Sanarwar ta bayyana cewa:

"Hankalinmu ya kai ga wani bidiyo da ya bazu na wasu mutane da ba a gane ko su waye ba suna zane wani Dan Bilki Kwamanda, inda ake zargin wakilan gwamnatin jihar Kaduna ne.
"Gwamnatin jihar Kaduna tana son nesanta kanta daga wannan mugun abu. Ba ya cikin dabi'armu. Irin wadannan ayyuka na dabbanci ba su da gurbi a cikin al'umma ta gari."

Gwamnati za ta binciki bidiyon Kwamanda

Kara karanta wannan

Yadda aka zane masoyin Buhari, Dan Bilki Kwamanda saboda 'zagin' Gwamnan Kaduna

Sanarwar ta cigaba da cewa, gwamnatin jihar Kaduna tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, tana aikin tukuru domin gina yarda da aminci tsakanin 'yan jihar.

"Gwamnatin tana karbar duk wani nau'in ra'ayi kuma ta samar da muhallin bunƙasar duk wata mahanga ta siyasa.
"Gwamnan a tsaye yake wurin yaƙi domin kare haƙƙin ɗan Adam da 'yancinsa. Ba zai taba saka wani ya ci zarafin wani ba saboda yana da ra'ayi mabanbanci a siyasa."

- A cewar sanarwar.

Gwamnan ya buƙaci a zurfaffen bincike game da wannan bidiyon domin gano tushen lamarin.

A karshe an ji Uba Sani ya kuma sanar da cewa ya shirya ganin cewa wadanda suka yi laifin sun fuskanci fushin hukuma.

Kannywood ta fusata da dukan Dan Bilki

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, jaruman masana'antar fim ɗin Hausa wanda aka fi sani da Kannywood, sun fusata da ganin bidiyon cin zarafin Dan Bilki Kwamanda.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jawo mutane a jiki, ya naɗa sababbin hadimai sama da 1,000

Nazifi Asnanic, mawaki kuma mai shirya fim, ya ce abin da aka yi wa mai sharhi kan lamuran siyasar ya saba dokar dimokuradiyyar Najeriya, inda ya ce hakan akwai takaici.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.