An Shiga Jimami Bayan An Tsinci Gawar Sojan Najeriya a Cikin Daki

An Shiga Jimami Bayan An Tsinci Gawar Sojan Najeriya a Cikin Daki

  • Wani sojan Najeriya da ya yi ritaya ya riga mu gidan gaskiya a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau a ranar Laraba, 17 ga watan Yulin 2024
  • Tsohon sojan mai suna Kanal BT Vandi an tsinci gawarsa ne a ɗakin baƙi na sansanin 'Defence Academy' da ke kan titin Vom a birnin Jos na jihar
  • An bayyana cewa wani ma'aikaci ne ya gano gawar ta sa bayan ya yi kwana ɗaya a cikin ɗakin da ya shiga a ranar Talata, 16 ga watan Yulin 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - An tsinci gawa wani sojan Najeriya da ya yi ritaya, mai suna Kanal BT Vandi, a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya Sake ɗauko mace, ya naɗa ta a shirgegen mukami a gwamnatin tarayya

An tsinci gawar marigayin ne a sansanin ‘Defence Academy’ da ke kan titin Vom, a birnin Jos.

An tsinci gawar tsohon soja a Plateau
An yi kacibus da gawar tsohon sojan Najeiya a Jos Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tsohon soja ya rasu a Jos

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa sojan mai ritaya ya rasu ne a ɗakinsa bayan ya shiga ciki da wasu ƴan sa'o'i kaɗan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce wani ma’aikaci ne ya tarar da gawarsa da misalin ƙarfe 3:20 na rana.

Jaridar Sahara Reporters ta ce ce marigayi Kanal Vandi ya shiga ɗakin baƙi na sansanin a ranar Talata, 16 ga watan Yuli, kuma an gano cewa ya mutu ne a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli.

Za a kai gawar marigayin zuwa asibitin rundunar sojoji ta uku da ke Jos domin gudanar da bincike kan gawarsa.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Sai dai, da aka tuntuɓi muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta uku ta sojojin Najeriya, Manjo Aliyu Danja, bai tabbatar da aukuwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

An kama ɗan Gwamna Zulum da zargin hallaka wani a gidan Gala a Indiya? Gaskiya ta fito

Ya bayyana cewa zai yi bincike kan rahoton domin tabbatar da hakan a hukumance.

Hafsan tsaro ya ba jami'an tsaro umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Laftanar Janar Christopher Musa, ya ba da sabon umarni ga kwamandojin hukumomin tsaro da ke yaƙi da satar man fetur a yankin Neja Delta.

Janar Christopher Musa ya umarce su da su kawo ƙarshen satar man fetur a yankin nan da makonni biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng