JAMB Ta Sanar da Sabon Mafi Karancin Makin Shiga Manyan Makarantu a Najeriya

JAMB Ta Sanar da Sabon Mafi Karancin Makin Shiga Manyan Makarantu a Najeriya

  • Hukumar zana jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta sanar da sabon mafi ƙarancin makin shiga jami'o'i a fadain Najeriya
  • Yayin da JAMB ta ayyana maki 140 matsayin mafi karancin, ta ce ba za ta tilastawa manyan makarantu amfani da makin ba
  • A zantawarmu da wakilin daliban Mani, daga jihar Katsina, Sanusi Ya'u Mani ya jinjinawa JAMB tare da aika sabuwar bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Alhamis ne masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi a Najeriya suka tsayar da maki 140 a matsayin sabon mafi ƙarancin makin samun gurbin karatu a jami'o'i.

Wannan makin da aka kayyade ba shi zai ba dalibi damar samun gurabin karatu a dukkanin jami'o'i ba, inji shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede.

Kara karanta wannan

JAMB Ta jero sunayen fitattun jami'o'i 5 da ake zargin su na aikata babban laifi a Najeriya

JAMB ta amince da mafi ƙarancin makin shiga jami'o'i da sauran manyan makarantu
JAMB ta amince da mafi ƙarancin makin shiga jami'o'i da sauran manyan makarantu
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta rahoto cewa, manyan makarantu da dama sun bayyanawa hukumar JAMB mafi ƙarancin makinsu a taron da suka gudanar yau a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafi karancin makin shiga manyan makarantu

Jami'ar Pan-Atlantic dake Legas, jami'ar Covenant dake Ogun, jami'ar Obafemi Awolowo dake Osun da jami'ar jihar Legas su ne kadai suka bukaci maki 200 zuwa sama.

Mista Oloyede ya ja kunnen 'yan Najeriya kan baza labaran cewa hukumar JAMB din ce ta ƙayyade mafi ƙarancin makin.

Shugaban ya ce an amince da mafi ƙarancin makin samun gurbi a kwalejojin ilimi, kimiyya da na fasaha ya zama maki 100, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Taron ya samu halartar ministan Ilimi, Tahir Mamman da shugabannin jami’oi, da na kwalejoji gami da magatakardu na manyan makarantu da sauran masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa ƴan ƙwadago alƙawari 1 bayan amincewa da albashin N70,000 a Aso Villa

An nemi JAMB ta rage kudin jarabawa

A zantawarmu da Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban hakimin Mani da ke jihar Katsina, ya ce rage makin shiga manyan makarantu da JAMB ta yi abin a yaba mata ne.

Sanusi Mani ya ce akwai dalibai masu hazaka amma kan samu rashin sa a wajen zana jarabawar su gaza ci gaba da karatu, wanda wannan ragin zai kawo karshen hakan.

Sai dai wakilin daliban ya roki hukumar JAMB da ta duba yiwuwar rage kudin jarabawar JAMB la'akari da halin matsin tattalina arziki da ake ciki a kasar.

Wakilin daliban ya ce iyaye da dama na fama da abin da za su ci a rana, inda wani gidan kan gaza cin abinci sau daya, balle ayi maganar biyan kudin JAMB din na yanzu.

JAMB ta gano masu digirin bogi

A wani labari na daban, hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu, JAMB, ta bayyana cewa ta gano wasu mutane 3,000 masu digirin bogi.

Kara karanta wannan

Jami'o'in Arewa 3 sun kafa tarihi a karon farko, sun samu kyautar miliyoyin kudi

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa, sun gano wasu mutane da ke ta ikirarin mallaka kwalin kammala digiri, bayan ba gaskiya bane ba.

Farfesan ya sanar da cewa, akwai wasu jami'o'i masu bada guraben karatu a Najeriya ba bisa ka'idar hukumar JAMB din ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.