Halin Kunci: 'Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu da Kaso Mai Yawa Saboda Talakawa

Halin Kunci: 'Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu da Kaso Mai Yawa Saboda Talakawa

  • Yayin da ake fama da shan wuya a Najeriya, 'yan Majalisar Wakilai sun rage albashinsu da 50% domin tallafawa talakawa
  • 'Yan Majalisar wakilan kasar sun dauki wannan matakin ne domin samar da sauki ga al'umma duba da halin kunci da ake ciki
  • Hakan ya biyo bayan kudirin mamban Majalisar, Isiaka Ayokunle da ke rokon masu zanga-zanga su janye daga kudirinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai a Najeriya ta zaftare albashin mambobinta domin tallafawa al'umma yayin da ake shan fama.

Mambobin Majalisar sun amince da rage 50% na albashinsu saboda tallafawa al'umma yayin da ake cikin halin ƙunci.

Majalisar Tarayya ta dauki mataki kan halin kunci da ake ciki
Majalisar Wakilai ta zaftare albashinta domin tallafawa al'umma. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Haƙin ƙunci: Majalisar Wakilai ta rage albashi

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya gamu da matsala bayan kayyade shekarun shiga manyan makarantu

Mataimakin kakakin Majalisar, Benjamin Kalu shi ya gabatar da bukatar a gaban Majalisar a yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ben Kalu ya ce akwai bukatar su rage albashinsu na N600,000 da 50% na tsawon watanni shida taimakawa mabukata a fadin kasar baki daya.

'Yan majalisar sun amince da rage albashin ne har na tsawon watanni shida domin tallafawa da taimakon marasa karfi a ƙasar, TheCable ta tattaro.

Tsadar rayuwa ya sa majalisa ta rage albashi

Wannan ya biyo bayan kudirin da mamban Majalisar, Isiaka Ayokunle ya kawo inda yake rokon masu zanga-zanga sun janye kudurinsu.

Ayokunle ya ce madadin zanga-zangar ya kamata su tattauna da gwamnati domin shawo kan matsalolin da ake fama da su a yanzu.

Benjamin Kalu ya ce hakan zai ba su damar taimaka wa Gwamnatin Tarayya wurin sanar da abinci a kasar domin saukaka halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Tinubu ya kayyade shekarun shiga manyan makarantu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fitar da sanarwa kan adadin shekarun da ake bukata kafin shiga manyan makarantu.

Gwamnatin ta umarci hukumar kula da jarabawa ta JAMB da ta tabbatar sai masu shekaru 18 za a ba gurbin karatu a Jami'o'i.

Wannan sabon umarni ya gamu da tirjiya bayan masu ruwa da tsaki sun ki amincewa da haka inda suka yi fatali da tsarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.