Bayan Hana Ma'aikata Albashin Watanni 4, Jami'an Tsaro sun Hana su Zanga Zanga

Bayan Hana Ma'aikata Albashin Watanni 4, Jami'an Tsaro sun Hana su Zanga Zanga

  • Rundunar 'yan sandan kasar nan sun dakile yunkurin kungiyar ma'aikatan manyan makarantu na gudanar da zanga zanga domin neman hakkinsu
  • Kungiyar ma'aikatan SSANNU da NASU sun shirya gudanar da zanga zanga a ranar Alhamis domin nuna fushinsu kan saba alkawarin gwamnati
  • Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Benneth Igwe ne da kansa ya isa filin Unity Fountain a Abuja inda ya ce ba a amince su yi zanga-zanga ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Jami'an tsaro a babban birnin tarayya Abuja sun hana hadakar kungiyar manyan ma'aikatan makarantu ta SSANNU da NASU gudanar da zanga-zanga a babban birnin.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Kungiyoyin sun shirya gudanar da zanga-zanga saboda nuna fushinsu kan yadda gwamnati ta hana su albashin watanni hudu.

SSANNU
Jami'an tsaro sun dakile yunkurin zanga-zanga Hoto: Majority World
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa shugabancin kungiyar na shirin yin bayani ga mambobinta a shirinsu na zuwa ma'aikatar ilimi da ta kwadago ne kwamishinan 'yan sanda, Benneth Igwe ya isa wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun dakile zanga zanga

Kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayya, Benneth Igwe ya shaida wa kungiyoyin ma'aikatan manyan makarantun kasar nan cewa ba a amince su gudanar da zanga-zanga ba.

Daga bisani rundunar ta rufe hanyoyin shige da fice daga Unity Fountain a babban birnin tarayyar da 'yan kungiyoyin su ka hallara.

Jaridar The Nation ta wallafa cewa duk kokarin da jagororin kungiyar su ka yi na neman a ba su dama su gudanar da zanga-zangar ya ci tura.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a PDP, ana neman tumbuke shugabar jam'iyya

Daga karshe dai shugabannin SSANNU da NASU su ka shiga motocinsu inda su ka nufi ma'aikatar ilimi da ta kwadago domin mika takardun kokensu ga ministocin ma'aikatun.

Ma'aikatan jami'a sun yi barazanar yajin aiki

A wani labarin kun ji cewa kungiyar ma'aikatan jami'a ta shirya tsunduma yajin aiki inda ta yi barazanar rufe jami'o'in kasar nan bisa kin biyan hakkokinsu da mahukunta su ka yi.

Kungiyar SSANU ta yi barazanar bayan cikar wa'adin mako biyu da su ka bawa gwamnati na ta cika alkawuran da ta dauka, ciki har da biyan hakkokin ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.