Gwamnonin PDP Sun Goyi Bayan NLC, Sun Faɗi Matsaya Kan Sabon Mafi Karancin Albashi
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana goyon bayan buƙatar kungiyar NLC na ƙarin mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
- A wata sanarwa da kungiyar gwamnonin ta fitar bayan taro a Enugu, ta buƙaci a yi la'akari da ƙarfin arzikin gwamnatoci kafin yanke adadin ƙarin
- Sanarwan ta bayyana cewa ma'aikata suna da haƙƙin neman a ƙara masu albashi duba da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnonin da suka hau mulki a inuwar jam’iyyar PDP sun ayyana goyon bayansu ga yunkurin da kungiyoyin kwadago ke yi na ganin an ƙara albashi.
Gwamnonin PDP sun bayyana matsayarsu ne a wata sanarwa da suka fitar jim kaɗan bayan kammala taro a jihar Enugu.
Rahoton The Cable ya hakaito gwamnonin na cewa ya zama wajibi a yi taka tsan-tsan da la'akari da duka matakan gwamnati wajen yanke sabon mafi ƙarancin albashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsu, ta haka ne kaɗai za a iya gane ƙarfin gwamnatoci wajen iya biyan kowane adadi aka cimma matsaya a kai, cewar rahoton Leadership.
Gwamnonin sun ce bukatar kungiyoyin ma’aikata na neman karin albashi “ta yi daidai” duba da halin matsin tattalin arzikin da al'umma suka wayi gari a ciki.
Gwamnonin PDP sun faɗi matsaya
"Duk da muna goyon bayan bukatar ma'aikata na ƙarin albashi amma ya kamata a duba ƙarfin arzikin ƙananan hukumomi, jihohi da tarayya wajen biyan kuɗin.
"Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan batun mafi karancin albashin, muna rokon kowane ɓangare ya mayar da wuƙarsa kube, ka da a yi abin da zai kawo karya doka da oda da uwa uba gurguntar da tattalin arziki.
- In ji gwamnonin PDP.
NLC ta aika saƙo ga majalisa
A wani rahoton na daban, an ji cewa yayin da matasan Najeriya ke yin barazanar shiga zanga-zanga a fadin kasar nan, kungiyar kwadago ta tura sabon sako ga majalisa.
Kungiyar kwadago ta gargadi majalisa kan shirin da Bola Tinubu yake yi na kai musu kudurin mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng