Sojoji Sun Cafke Masu Tayar da Fitina a Filato, Sun Kama Tulin Makamai

Sojoji Sun Cafke Masu Tayar da Fitina a Filato, Sun Kama Tulin Makamai

  • Rundunar sojin Najeriya ta fitar da rahoto bayan shafe kwanaki tana farautar miyagu masu tayar da fitina a jihar Filato
  • Hakan ya biyo bayan kisan gilla da miyagun suka yi wa wani jami'in shige da ficen Najeriya ne a lokacin da suke kwantar da tarzoma
  • Rundunar sojin ta samu nasarar cafke bata gari tare da kwato tarin makamai da suke amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu bayan fita samame na mako guda kan yan bindiga.

Rundunar ta sanar da cewa ta kama wadanda ake zargi da tayar da fitina a jihar da kuma kwato makamai a wajensu.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya tsallake rijiya da baya, iyalansa 3 sun mutu a gobara

Sojojin Najeriya
Sojoji sun kama miyagu a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro yadda aka kama miyagun ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da sojoji suka kama a Filato

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cakfe yan ta'adda takwas a karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

Ana zargin yan ta'addar ne da aikata kisan jami'an shige da ficen Najeriya mai suna Christopher Luka da aikata wasu laifuffuka.

Filato: Makaman da sojoji suka kwato

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kwato bindigogi kirar AK47 guda 12 da tarin makamai wajen yan ta'addar.

Haka zalika sojojin sun kwato babur guda bakwai da ake zargi miyagun na amfani da su wajen kai hare hare.

Sojoji na neman miyagu ruwa a jallo

Har ila yau rundunar sojin ta ce tana neman Timothy Zakka, Sam P, Dachum Job da Yakubu Ishaku ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Rundunar ta bukaci dukkan waɗanda suke da bayanai kan yadda za a kama mutanen su sanar da ita cikin gaggawa.

Sojoji sun kashe yan bindiga a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar Taraba a Arewa maso gabas.

Wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane ya sheka lahira a karamar hukumar Wukari bayan sun yi mummunan fada a tsakaninsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng