Gwamna Ya Gano Abin da Ya Ta'azzara Matsalar Rashin Tsaro
- Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya danganta matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar kan ta'ammali da miyagun ƙwayoyi
- Gwamna Buni wanda ya koka kan matsalar ya buƙaci iyaye da su riƙa tona asirin ƴaƴansu waɗanda ke da ɗabi'ar shan miyagun ƙwayoyi
- Ya kuma umarci sarakunan gargajiya da su tashi tsaye wajen wayar da kan jama'a dangane da matsalar ta'ammali da kayayyakin masu sanya maye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar.
Gwamna Buni ya danganta matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar kan ƙaruwar shan miyagun ƙwayoyi.
An ƙaddamar da shirin gyaran hali a Yobe
Gwamna Buni ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama'a mai taken “Operation Gyaran Hali” wanda ma’aikatar kula da harkokin addini da ɗa’a ta shirya a Damaturu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce, duk da cewa an fatattaki ƴan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, amma duk da haka suna kai ƙananan hare-hare a ƙauyukan da ke kan iyaka da dajin Sambisa.
A cewarsa, rikicin manoma da makiyaya ya kuma ta’azzara saboda ƙaruwar shan miyagun ƙwayoyi a jihar.
Gwamnan ya ce lamarin yana da matuƙar tayar da hankali kuma ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa domin daƙile matsalar.
Gwamna Buni ya samar da mafita
Gwamna Buni ya buƙaci iyaye da su fallasa ƴaƴansu da ke harka da miyagun ƙwayoyi.
Ya umarci sarakunan gargajiya da su ci gaba shirye-shiryen wayar da kan jama’a da kuma goyon bayan gwamnati a yaƙin da take yi kan ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.
Gwamna Buni ya rantsar da kwamishinoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rantsar da kwamishinoni biyu, shugaban ma’aikata da manyan sakatarori hudu.
Gwamna Buni ya kuma rantsar da masu ba da shawara na musamman guda 28 domin gudanar da ayyuka masu inganci a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng