Gwamnatin Abba Gida Gida ta Kinkimo Ayyukan Biliyoyi Domin Inganta Rayuwar Talakan Kano
- Gwamnatin Kano ta ware makudan biliyoyi da za ta yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya kasa
- Za a wanzar da ayyukan nan ne a kananan hukumomin birane da karkara guda 44 da ake da su a jihar ta Kano
- Darakta janar kan yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware Naira Biliyan 29 domin gudanar da ayyukan raya jihar Kano. An ware adadin kudin ne domin aiwatar da sababbin manyan ayyuka da kammala wasu da aka fara tun a can baya.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da daraktan yada labarai ga gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na X.
Ayyukan da za a yi a Kano
Gwamnatin Kano za ta gudanar da manya-manyan ayyuka domin bunkasa ayyukan mazauna jihar. Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ke magana da yawun gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Manyan ayyuka da za a gudanar sun hada da;
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Aikin tituna
Majalisar zartarwa ta Kano ta amince da fitar da N7, 761,681,223.22 domin aikin tituna masu tsayin kilomita 4. Gwamnatin Kano ta fitar da 10% kudin, za a yi aikin ne hadin gwiwa da kananan hukumomi 44 bisa kason 30:70.
2. Sayo tiransifoma 500
Gwamnatin Kano ta ware N7,123,750,000.00 domin sayo tiransifoma da za a raba ga kananan hukumomi. Tiransifoma 500 za a raba ga yankunan da ke kananan hukumomin Kano 44 a wani yunkuri na inganta harkar wutar lantarki.
3. Aikin mazabu
Haka kuma an ware N6,400,000,000.00 domin gudanar da ayyuka a mazabun jihar. Ana sa ran ayyukan za su taimaka wajen kai ci gaba karkara.
4.Biyan ma'aikatan REMASAB a Kano
N130,460,000.00 majalisar zartarwar Kano ta ware domin biyan ma'aikatan wuce gadi da ke sharar titunan jihar. Ma'aikatan 2,803 ne ake sa ran za a biya da kudin.
5. Gyara da fentin shingayen kare hadurra
Gwamnatin Abba Gida-Gida ta ware N248,789,369.72 wajen gyara wa da yi wa shingen kare afkuwar hadurra a titunan Kano.
Kano: Gwamnati za ta yi wasu ayyuka
A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin Kano ta dauko manyan ayyuka domin inganta rayuwar mazauna birane da karkarar da ke jihar.
Daga cikin ayyukan akwai gina tituna a karkara domin habaka noma, sayen motoci hilux da kuma biyan wani kaso na basussukan da ake bin gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng