Ndume: Daurawa Ya Nuna Fargaba Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Fadi Illar Haka Gare Su
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da mulki a wannan gwamnatin ta Bola Tinubu
- Daurawa ya nuna fargaba kan yadda ake dakatarwa ko korar wadanda suke kokarin fadar gaskiya game da halin da ake ciki
- Malamin ya ce abin tsoro ne matuka wadanda suke zaton za su jagorance su wurin Tinubu ana daukar irin wannan mataki kansu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya nuna fargaba kan gwamnatin Bola Tinubu.
Malamin ya ce abin ya fara ba shi tsoro ganin yadda ake gudanar da gwamnatin a yanzu duk da halin da ake ciki.
Daurawa ya fara firgita da mulkin Tinubu
Shehin malamin ya bayyana haka da safiyar yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daurawa ya ce lamarin kasar ya fara ba shi tsoro musamman yadda ake kora ko dakatar da wadanda suke sa ran yi musu jagoranci zuwa fadar shugaban kasa.
Ya ce abin da ya faru ya firgita shi inda ya ce anya kuwa akwai adalci ko tausayin talakawa a zukatan shugabanni.
"Abin da ya faru ya ba ni tsoro."
"Irin mutanen da muke fata za su yi mana jagotanci zuwa wurin shugaban kasa domin isar da sakon al'umma an fara korasu da dakatar da su daga mukamansu."
"An yi haka ne saboda sun koka kan halin da ake ciki, anya kuwa akwai tausayi da adalci a cikin zukatansu kan talakawa?"
- Aminu Ibrahim Daurawa
An dakatar da Sanata Ndume daga mukaminsa
Wannan martani na Daurawa bai rasa nasaba da dakatar da Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban masu tsawatarwa a Majalisar.
Majalisar ta dakatar da Ndume bayan ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ganin yadda ake cikin halin kunci.
'Yan Majalisa sun ki hukunta Ndume
Kun ji cewa mambobin Majalisar Dattawa da dama sun ki amincewa da bukatar hukunta Sanata Ali Ndume daga jihar Borno.
Sanatocin Majalisar sun yi tawaye kan bukatar hukunta Ali Ndume bayan ya fadi munanan kalamai gare su bayan an dakatar da shi.
Sanata Fasuyi Cyril da ke wakiltar Ekiti ta Arewa shi ya bukaci hukunta Ndume inda sanatoci suka hada baki da kin amincewa da haka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng