Abba Kabir Yusuf Ya Fara Muhimman Ayyuka 10 da Za Su Shafi Talakawa a Kano
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki damarar yin wasu muhimman ayyuka guda 10 domin kawo cigaba a Kano
- Mai girma Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a yau Laraba bayan zaman majalisar zartarwar jihar Kano
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta tatttaro muku jerengiyar ayyukan da wuraren da za a aikata su a sassan Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Abba Kabir Yusuf ya dauki aniyar gabatar da wasu muhimman ayyuka guda 10 a jihar Kano.
Gwamna Abba ya amince da yin ayyukan ne a zaman majalisar zartarwar jihar Kano na yau Laraba.
Legit ta tatttaro muku cikakken bayani a kan jerin ayyukan da gwamnatin ta shirya yi a faɗin jihar Kano kamar yadda gwamna Abba ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayyuka 10 da Abba Kabir zai yi
- Cigaba da ayyukan tituna masu hannu biyu kuma masu tsawon kilo mita biyar a dukkan ƙananan hukumomin jihar Kano.
- Gabatar da ayyukan tituna a kauyukan ƙananan hukumomin Gwale, Ajingi da Kiru/Madobi wanda za su lashe sama da Naira miliyan 239.
- Gudanar da ayyuka na musamman a mazabun jihar Kano da za su laƙume kudi sama da Naira biliyan 6.
- Gudanar da aikin hanya wacce ta fara daga kwanar Gammawa a karamar hukumar Gezawa a kan kudi sama da Naira miliyan 343.
- Sayen motoci guda 20 kirar Toyota Hilux da mota kirar bas guda daya ga ma'aikatun gwamnatin jihar.
- Biyan kason kudi wajen yin ayyukan titi a karkara domin inganta harkar noma da tattalin arziki a kauyuka wanda zai laƙume sama da Naira biliyan 5.
- Gyara da samar da ofishin kwamitin ko-ta-kwana domin hana satar waya a gidan gwamnatin jihar.
- Gyara kan tituna daban daban na cikin birnin Kano da ke kusa da kofar Nasarawa a kan kudi kimanin Naira miliyan 29.
- Biyan kashi 30% na kudin ayyukan hanya da da za a yi a kananan hukumomin jihar guda 44 a kan sama da Naira miliyan 354.
- Biyan kudin alawus na ma'ikatan masu sharar hanya a Kano su 2,803 wanda ya haura Naira miliyan 130.
Abba zai inganta lantarki a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa a zaman majalisar zartarwar jihar Kano na 16, gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin da zai kawo ingantar wutar lantarki.
Hakan na zuwa ne bayan samun tangarɗa da ake yawan yi a harkokin wutar lantarki wanda ke shafar sana'o'i da ayyukan al'ummar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng