Kofar Mata: Abba Kabir, Kwankwaso Sun Tura Sako ga Kwamishina Bayan Iftila’in Gobara

Kofar Mata: Abba Kabir, Kwankwaso Sun Tura Sako ga Kwamishina Bayan Iftila’in Gobara

  • Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da Rabiu Kwankwaso sun jajantawa kwamishinan ilimi mai zurfi, Yusuf Kofar Mata
  • Gwamnan da mai gidansa sun tura sakon ta'aziyya ga kwamishina game da rasa iyalansa uku bayan itfila'in gobara a gidansa
  • Lamarin ya faru ne a yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024 inda ya rasa 'yarsa da yayarsa da kuma matar dan uwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan kwamishinan ilimi mai zurfi, Yusuf Kofar Mata.

Gwamnan Kano ya jajantawa kwamishinan kan iftila'in gobara da ya afku a gidansa da ya yi sanadin mutuwar mutane uku.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki matakin inganta wutar lantarki a jihar Kano, Abba zai kashe N7.1bn

Kwankwaso da Gwamna Abba sun jajantawa kwamishinan Kano bayan gobara a gidansa
Gwamna Abba Kabir da Rabiu Kwankwaso sun tura sakon ta'aziyya ga kwamishinan Kano, Yusuf Kofar Mata kan gobara a gidansa. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Abba Kabir ya jajantawa kwamishina kan gobara

Abba Kabir ya bayyana haka ne da yammacin yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Inna Lillahi wa inna ilayhi rajiun."
"Na kadu da samun labarin rasuwar iyalan kwamishinan ilimi mai zurfi, Yusuf Kofar Mata har guda uku a iftila'in gobara."
"Daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai 'yarsa Maimuna (Islama) da yayarsa, Hajiya Khadija da kuma matar dan uwansa, Hajiya Juwairiyya."
"Ina addu'ar Allah ya sanya su gidan aljanna Firdaus, muna jajanta masa a irin wannan yanayi da yake ciki da iyalansa."

- Abba Kabir

Kwankwaso ya kadu da iftila'in gobara

Sanata Rabiu Kwankwaso shi ma ya tura sakon ta'aziyya a shafinsa na X bayan faruwar iftila'in.

"Ina mika sakon ta'aziyya ga kwamishinan ilimi mai zurfi a Kano, Yusuf Kofar Mata bayan rasa 'yarsa, Maimuna da yayarsa, Hajiya Khadija da kuma matar dan uwansa, Hajiya Jiuwairya a iftila'in gobara."

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya tsallake rijiya da baya, iyalansa 3 sun mutu a gobara

"Ba ni da wasu kalmomi da zan iya fada kan wannan iftila'i amma mun mika komai ga Ubangiji."
"Muna addu'ar Ubangiji ya sanya su gidan aljanna Firdausi."

- Rabiu Kwankwaso

Kano: Kwamishina ya yi asara a gobara

Kun ji cewa an samu mummunar gobara a gidan kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Dakta Yusuf Kofar Mata.

Rahotanni na nuni da cewa gobarar ta yi barna sosai ciki har da asarar rayukan 'yarsa da yayarsa da matar dan uwansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.