A Tashin Farko, Sabon Sarkin Karaye ya Jaddada Mubaya'a ga Sarki Sanusi II a Kano
- Sabon sarkin Karaye, Muhammad Mahraz ya ziyarci fadar Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a yau Laraba
- Ziyarar na zuwa ne bayan babbar kotun jiha ta tabbatar wa da Sarki Sanusi mulkinsa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nada shi
- Sarkin na Karaye ya jaddada cewa su masu biyayya ne kuma ba za su bijirewa umarnin magabatansu ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sabon sarkin Karaye, Muhammad Maharaz ya ziyarci fadar sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II kwana daya da nada shi.
A ranar Talata ne gwamnatin Kano ta nada sababbin sarakuna a masarautun Karaye, Gaya da Rano a matsayin sarakuna masu daraja ta biyu.
A bidiyo da @AmeerNaira ya wallafa, an gano Sarkin na karaye ya na jaddada mubaya'a ga sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba za mu yi butulci ba," Sarkin Karaye
Sarkin Karaye, Muhammad Maharaz ya shaida wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II cewa ba za su yi butulci ga gidan dabo ba.
Sabon nadadden sarkin ya bayyana haka ne a ziyarar mubaya'a da su ka kai fadar Sarkin Kano, inda ya ce za su ci gaba da mutunta dokar kasa, kamar yadda ake gano a bidiyon da Sa'adatu Baba Ahmad ta wallafa.
"Da kuma tabbatar wa da mai martaba sarki cewa wannan canji na zamani da aka kawo ba zai sa mu butulce wa wannan gida da shi ne iyaye da kakanni mu ka gada ba."
"Idan mu ka yi haka mun raina girma da Allah ya ba su."
- Sarkin Karaye, Muhammad Mahraz
Sarkin Karaye ya jaddada wa sarkin cewa ba za su bar gidansu na dabo ba, tare da addu'ar Allah ya yi wa sarkin jagora, tare da yi wa Kano addu'ar zaman lafiya.
Majalisa ta amince da kirkirar masarautu
A baya mun ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kirkirar sababbin masarautu.
Masarautun da aka kirkira guda uku sun hada na Rano da Gaya da kuma Karaye wanda za su kasance masu daraja ta biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng