Sarautar Kano: 'Dan PDP Ya Fadi Yadda Abba Yake Nadamar Daukar Wasu Matakai

Sarautar Kano: 'Dan PDP Ya Fadi Yadda Abba Yake Nadamar Daukar Wasu Matakai

  • Yayin da ake ci gaba da rigimar sarautar Kano, wani 'dan jam'iyyar PDP ya magantu kan matakan da Abba Kabir Yusuf ya ke dauka
  • Abdul-azizi Na'ibi Abubakar ya ce gwamnan ya dauki matakai da dama amma yanzu yana nadama yayin da yake komawa kansu
  • Jigon PDP ya ce gwamnan ya yi rusau amma kuma ya biya diyya yayin da ya rushe masarautu yanzu ya kirkiri wasu a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wani 'dan jam'iyyar PDP, Abdul-aziz Na'ibi Abubakar ya caccaki yadda Gwamna Abba Kabir ke gudanar da mulki.

Abdul-aziz Na'ibi ya ce abin takaici ne yadda gwamnan ya yi rusau sannan kuma ya zo daga baya yana biyan diyya a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kofar Mata: Abba Kabir, Kwankwaso sun tura sako ga kwamishina bayan iftila'in gobara

Jigon PDP ya caccaki Abba Kabir kan matakan da ya ke dauka a Kano
Jigon PDP ya bayyana yadda Abba Kabir ke nadamar aikata wasu ayyuka a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf.
Asali: UGC

Dan PDP ya dura kan gwamna Abba

Daraktan yada labaran na kungiyar Atiku Light Organization ya fadi haka ne a shafinsa na X a ranar Laraba 17 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdul-aziz Na'ibi ya ce duka matakan da gwamnan ke dauka a jihar ya zo yana nadama saboda gidan jiya yake komawa.

Wannan na zuwa ne bayan Abba Kabir ya sake kirkirar masarautu guda 3 a jihar duk da kalubalantar matakin Abdullah Ganduje a baya.

Masarautu 3 da aka kirkira a Kano

Daga cikin masarautun akwai Rano da Gaya da kuma Karaye sai dai babu Bichi da kuma Wudil a cikin wadanda aka kirkiran.

Majalisar jihar ce ta amince da kirkirar masaurautun guda uku masu daraja ta biyu wadanda za su kasance karkashin Sarki Sanusi II.

"Ka rushe kadarori da dukiyar al'umma, amma daga baya ka zo ka na biyan diyya."

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki matakin inganta wutar lantarki a jihar Kano, Abba zai kashe N7.1bn

"Ka rushe masarautun jihar Kano da nufin cewa kana son dawo da martabarsu, yanzu kana nadama kuma ka sake kirkirar wasu masarautu."
"Kusan duka matakan da ka dauka ka na nadamar aikata su."

- Abdul-aziz Na'ibi Abubakar

Dan Agundi ya soki Kwankwaso kan masarautu

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya yi magana kan masarautun jihar Kano.

Dan Agundi ya soki Sanata Rabiu Kwankwaso inda ya ce ya tafka babban kuskure tun farko wurin dawo da Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.