An Umarci 'Yan Arewa Su Fice Daga Jihar Delta, Dattawan Yankin Sun Yi Martani

An Umarci 'Yan Arewa Su Fice Daga Jihar Delta, Dattawan Yankin Sun Yi Martani

  • Wata masarauta a jihar Delta ta ba 'yan Arewa mazauna yankin wa'adin kwanaki hudu da su bar garin
  • Sarkin Hausawan yankin masarautar Abavo, Usman Alhassan ya ce da yawa daga mazauna yankin ma ba su da na abinci
  • Amma kungiyar ACF ta manyan Arewa ta shaidawa Legit cewa za su tuntubi gwamnatin Delta da jami'an tsaro kan al'amarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta - Wata masarauta a jihar Delta ta umarci 'yan Arewa da ke zaune a yankin su gaggauta barin garin cikin wasu kwanaki.

Masarautar Abavo ta bayar da wa'adin kwanaki hudu ga 'yan Arewa mazauna yankin, wanda ya fara daga ranar Litinin kuma zai kare a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Delta State Government
An bawa 'yan Arewa wa'adin kwanaki 4 su fice daga yankin Delta Hoto: Delta State Government
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Sarkin Hausawan yankin, Usman Alhassan ya ce ba zato ba tsammanin aka aika masu da wa'adin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu kudin motar komawa Arewa," Sarkin Hausawa

Sarkin hausawa mazauna masarautar Abavo, Usman Alhassan ya ce wasu daga cikin 'yan Arewa a yankin ba su da kudin motar da za su dawo jihohinsu.

Wannan na zuwa ne bayan masarautar yankin ta ba su kwanaki hudu da su tattara nasu ya nasu su bar garin, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Usman Alhassan ya kara da cewa yanzu haka wasu ba su da kudin abinci, ballantana har su tattaro kudin mota cikin kwanaki hudu zuwa jihohinsu.

Dattawan Arewa sun yi martani

Kungiyar ACF ta Arewa ta ce wa'adin barin yankin jihar Delta abin tashin hankali ne, kuma ya saba doka.

Shugaban kungiyar, Dakta Faruq Umar ya shaidawa Legit cewa idan ana zargin wasu da aikata laifuffuka, kamata ya yi a a kai su ga hukuma.

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

Dakta Faruq Umar ya ce za su nemi jami'an tsaro da gwamnan Delta wajen kare rayuwar 'yan Arewa a can.

Ya yi alkawarin taimaka wa 'yan Arewa mazauna garin da kudin mota matukar aka tuntube su domin su dawo gida cikin mutunci.

'Yan kasuwar Arewa sun yi barazana

A baya mun ruwaito cewa dillalai da ke safarar kaya zuwa Kudu sun yi barazanar daina kai kaya yankin saboda rashin tsaro.

Shugabannin kungiyar da ke kai tumatir yankin Kudancin kasar nan sun yi zargin tsageru na jawo masu asara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.