Rano, Karaye, Gaya: Muhimman Abubuwa 3 Masu Muhimmanci Game da Sababbin Masarautun Kano

Rano, Karaye, Gaya: Muhimman Abubuwa 3 Masu Muhimmanci Game da Sababbin Masarautun Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kirkiri masarautu uku masu sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Rano, Karaye da Gaya
  • Sarakunan da za a nada za su kasance karkashin babban Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a yadda aka tsara
  • Sarakunan masu daraja ta biyu zasu nemi shawarar Sarkin Kano kan rikicin yanki, lamurran addini da sauransu a duk lokacin da hakan ta taso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - A ranar Talata ne majalisar jihar Kano ta amince da kirkirar sababbin kananan masarautu uku a jihar kuma Gwamna Abba Yusuf na jihar ya sa hannu a kai.

Sai dai, har zuwa lokacin da ya saka hannu a kan dokar kirkirar masarutun masu daraja ta biyu, bai bayyana sunan sarakunan da za su jagoranci masarautun ba.

Abba Yusuf ya mika takardar kama aiki ga sababbin sarakunan Kano
Abubuwan da ya kamata ku sani game da sababbin masarautun Kano. Hoto: @SanusiBature
Asali: Twitter

Sunayen sababbin sarakunan da aka nada

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Gwamna Abba Kabir ya kirƙiro sababbin masarautu 3 a jihar Kano

Sai a safiyar Laraba, 17 ga watan Yuli, Sanusi Bature Dawakin Tofa, daraktan watsa labaran gwamnan ya fitar da sanarwa a shafinsa na X mai dauke da sunayen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Dawakin Tofa ta ce:

"Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da nadin sarakuna uku masu daraja ta biyu.
"Sarakunan su ne: Alhaji Muhammad Mahraz Karaye (Sarkin Karaye), Alhaji Muhammad Isa Umar (Sarkin Rano) da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya (Sarkin Gaya).
"Wannan nadin zai fara aiki nan take."

Muhimman abubuwa game da masarautun Kano 3

Ga wasu abubuwa guda uku da ya kamata ku sani game da sabbin masarautun Rano, Gaya da Karaye da aka kirkira masu matsayin na biyu:

1. Shiyyoyin da ke karkashin masarautun

Kamar yadda rahoton The Cable ya nuna, masarautun Rano za ta kasance tana da shiyyoyin Bunkure, Rano da Kibiya a karkashinta yayin da shiyyoyin Karaye da Rogo ke karkashin masautar Karaye.

Kara karanta wannan

Majalisar Kano ta amince da kirkirar masarautu 3 karkashin Sarki Sanusi II

An tsara cewa masarautar Gaya za ta kunshi shiyyoyin Gaya, Albasu da Ajingi; yayin da duka masarautun biyu ke karkashin ikon babbar fadar jihar.

2. Sanusi II ne shugaban sarakunan 3

Sarakunan masu daraja ta biyu a jihar Kano za su kasance karkashin Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.

3. Sarakunan za su nemi shawarar Sanusi II

Sarakunan sababbin masarautun za su nemi shawarar Sarkin Kano Malam Sanusi II a lamurran da suka shafi jama'a, rikicin iyakoki, rikicin al'umma da al'amuran addini a dukkan yankunan su.

Gwamna Abba ya nada sabbin sarakuna

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa, zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada sabbin sarakuna a masarautu uku da ya sake kirkirowa a jiharsa.

Gwamnan ya bayyana sarakunan ne bayan rattaba hannu da yayi kan sabuwar dokar kirkirar masarautun a ranar 16 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.