'Yan Bindiga Sun Sako Mahaifiyar Mawaki Dauda Kahutu Rarara, Bayanai Sun Fito
- Bayan shafe akalla kwanaki 20 a hannun 'yan bindiga, mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ta samu 'yanci
- Mawaki Rarara ne da kansa ya fitar da sanarwar kubutar mahaifiyarsa daga hannun 'yan bindigar a safiyar ranar Laraba
- Sai dai Rarara bai yi wani ƙarin bayani game da yadda aka sako mahaifiyarsa ba, bayan rahoto ya nuna 'yan bindigar sun nemi kudin fansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa 'yan bindiga sun sako mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara bayan shafe akalla mako 2 a tsare.
A ranar Juma'a, 28 ga watan Yunin 2024 muka ruwaito cewa 'yan bindiga sun kutsa sabon gidan Rarara da ke gabashin Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja inda suka sace mahaifiyarsa.
'Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara
Fitaccen mawakin, Rarara ne ya sanar da kubutar mahaifiyarsa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a safiyar ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rarara ya ce:
"Cikin yarda da amincin Ubangiji mun samu dawowar mama cikin aminci."
Mawakin ya kuma mika godiya ta musamman ga abokan sana'arsa da ma masoyansa baki daya bisa irin kulawar da suka nuna masa da taya shi alhinin sace mahaifiyarsa da aka yi.
Sai dai Dauda Kahutu Rarara bai yi wani ƙarin bayani ba game da yadda aka sako mahaifiyarsa, da kuma bayyana ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin sakinta.
Mai magana da yawun Rarara a kafofin watsa labarai, Rabi'u Garba Gaya, ya wallafa bidiyon Rarara tare da mahafiyarsa bayan kubutarta.
Kalli bidiyon a nan kasa:
An nemi kudin fansar mahaifiyar Rarara
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindigan da suka sace mahaifiyar Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara sun faɗi kuɗin fansan da za a ba su.
An ce 'yan bindigan sun buƙaci da a biya su Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Hajiya Halima Adamu wacce suka sace a Kahutu.
Bayan sun bayyana kudin da suke so, sun kuma ba iyalan Hajiya Halima tabbacin cewa tana cikin ƙoshin lafiya sannan za a sake ta da zarar an biya kuɗaɗen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng