Zamfara: Mata 5 Sun Tsere Daga Hannun ’Yan Bindiga, an Yi Jana’izar Wasu Mutum 5
- Mutane biyar daga cikin wadanda 'yan bindiga suka sace a Zamfara sun yi nasarar kubuta daga hannun miyagun
- Kamar yadda sakataren dagacin Dan Isa ya bayyana, an yi jana'izar wasu mutane biyar da 'yan bindigan suka halaka
- Daya daga cikin wadanda suka tsira, ta ce dukan tsiya 'yan bindiga suka yi musu bayan sun dauke su a babura
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Mata biyar har da mai goyon jinjirin wata shida da aka sace a kauyen Dan Isa da ke karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara sun tsere daga hannun 'yan bindiga.
Sakataren dagacin kauyen Dan Isa, Malam Hassan Isa, wanda ya tabbatar da wannan cigaban a ranar Talata, inda ya ce sun koma kauyen ne a ranar Litinin.
A ranar Talata, jaridar Daily Trust ta bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hare-hare a kauyuka masu yawa a jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Hassan wanda aka fi sani da Yarima, ya ce:
"Wadanda suka gudo daga wurin 'yan bindigan sun hada da Na'imah Bashar da jaririnta Sudais Bashar, Safiya Isau, Inno Lawal Mai Rona, Samira da matar Alhaji Mukhtar Sani."
'Yan bindiga sun kashe mutane 5
Yarima ya ce adadin wadanda 'yan bindigar suka kashe zuwa yanzu ya kai mutum biyar sakamakon an samu wata karin gawa a daji.
A cewar Yarima:
"Da farko mun samu gawarwakin Sabi'u Daudu, Haruna Akyarkyara, Abdulmutalib Rabiu da Bashar Idris a sa'o'in farko na ranar Litinin. Da yamma muka samu ta Zaharadeen Aliyu
"A halin yanzu an tabbatar da cewa sun yi garkuwa da mutane 99 a ranar Lahadi, amma har yanzu muna rubuta sunayen saboda sun kai farmakin kauyuka daban-daban ne."
"Yadda na samu nasarar kubuta" - Mai goyo
A yayin bayyana abin da ta fuskanta, Na'imah da ta gudo daga hannun 'yan bindigar ta bayyana cewa fadowa tayi daga babur din da ke dauke da ita tare da danta na goye.
Malama Na'imah ta ce:
"Yan bindigan sun yi mana duka kuma suka ja mu suka dora a babura. Maza biyu da aka sace an harbesu, daya harsashi ya gogi kansa sai dayan a ciki.
"Ina mika godiya ga Allah, abin da kawai zan iya cewa kenan. Domin shi ya ba ni ikon tserowa."
'Yan bindiga sun sace mutum 150
A wani labari na daban, mun bayyana muku yadda 'yan bindiga suka shiga garin Dan Isa mai tazara kadan daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Miyagun sun ci karensu ba babbaka na tsawon awanni shida sannan suka halaka jama'a tare da yin garkuwa da wasu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng