Tsadar Rayuwa: Ibo Sun Dauki Matsaya Kan Shiga Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu
- A yayin da aka shirya gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kungiyar kabilar Igbo sun dauki matsaya
- Babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya ce ba batun tattalin arzikine ya dame su a halin yanzu ba
- Kungiyar ta ce abu mafi damun Igbo a yanzu shi ne a sako Nnamdi Kanu ba wai su shiga wata zanga-zangar adawa da gwamnati ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A ranar Tatalata ne kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta ce kabilar Igbo ba za ta shiga zanga-zangar da za a yi a fadin kasar nan ba da aka shirya yi daga 1 zuwa 10 ga Agustan 2024.
Ohanaeze Ndigbo, ta ce Igbo ba za su yi zanga-zangar adawa da Shugaba Bola Tinubu ba kan tabarbarewar tattalin arziki, tashin farashin kayayyakin masarufi da man fetur.
Jaridar Tribune ta ruwaito Mazi Okechukwu Isiguzoro, babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo karkashin tsagin Chidi Ibeh, ya ce yanzu kan mage ya waye a kabilar Igbo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Igbo ba za su shiga zanga-zanga ba
A wata sanarwa da ya fitar a Abakaliki, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya bayyana cewa ba za su shiga zanga-zangar ba saboda an dade ana amfani da Igbo matsayin karnukan farauta.
Mazi Okechukwu ya ce ana hantarar Igbo kan rashin tsaro a Kudu maso Gabas, yayin da kuma aka ki sakin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Ya yi nuni da cewa zanga-zanga da suka faru a baya sun yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin Igbo da dama ba tare da kabilar ta cimma wata nasara ba, jaridar The Punch ta ruwaito.
Abin da ya damu kabilar Igbo yanzu
Sanarwar ta jaddada cewa abin da ya fi damun yankin Kudu maso Gabas shi ne sakin Kanu, ba wai shiga wata zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar ba.
Sanarwar ta kara da cewa, Ohanaeze na bayar da cikakken goyon baya ga gwamnonin Kudu maso Gabas wajen ganin an samar da isassun matakan tsaro a lokacin zanga-zangar.
Don haka mai magana da yawun kungiyar ya bukaci 'yan kabilar Igbo na yankin da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum a watan Agustan 2024.
Zanga-zanga: Malamai sun gana da Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa al'ummar Najeriya da dama sun zargi malaman addinin Musulunci da ganawa da gwamnati domin hana zanga zanga.
Sai dai wani malami, Aliyu Muhammad Sani ya bayyana abin da suka tattauna yayin da suka gana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng