Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Lokacin Sauraron Kararrakin Masarautar Kano

Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Lokacin Sauraron Kararrakin Masarautar Kano

  • Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta shirya fara sauraron ƙararrakin da ke gabanta kan rikicin masarautar Kano
  • Shugabar kotun ɗaukaka ƙara, mai shari'a Monica Dongban-Mensem ta kafa kwamiti mai alƙalai uku da zai saurari ƙararrakin guda huɗu
  • Kotun ɗaukaka ƙarar za ta fara sauraron ƙararrakin ne kan rikicin na masarautar Kano a ranar Laraba, 17 ga watan Yulin 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja za ta saurari ƙararraki huɗu da ke gabanta kan rikicin masarautar Kano.

Kotun za ta saurari ƙararrakin ne a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli kan hukunce-hukuncen da babbar kotun tarayya da ke Kano da babbar kotun jihar Kano suka zartar.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Gwamna Abba Kabir ya kirƙiro sababbin masarautu 3 a jihar Kano

Kotun daukaka kara za ta saurari shari'ar masarautar Kano
Kotun daukaka kara za ta saurari kararrakin masarautar Kano ranar Laraba Hoto: Masarautar Kano, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

Kotu za ta zauna kan rikicin masarautar Kano

Shugabar kotun ɗaukaka ƙara, mai shari'a Monica Dongban-Mensem, ta kafa kwamitin alƙalai uku waɗanda za su saurari ƙararrakin da aka shigar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu shigar da ƙarar su ne gwamnatin jihar Kano da Antoni Janar na jihar, majalisar dokokin jihar da kakakinta, sai ƙarar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ɗaukaka.

Masu ɗaukaka ƙarar na ƙalubalantar hukuncin mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman wanda ya soke matakan da gwamnatin Kano ta ɗauka wajen aiwatar da sabuwar dokar masarautun jihar Kano.

Masu ɗaukaka ƙarar a ranar 14 ga watan Yuni sun buƙaci kotun da ta saurari ƙarar tare da yin watsi da ƙarar mai lamba FHC/KN/CS/182/2024 wacce ta ƙalubalanci soke masarautun na Kano.

Sarki Aminu Ado Bayero ya ɗaukaka ƙara ne kan hukuncin da mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun jihar ta yanke wanda ya umarci a kore shi daga fadar Nasarawa tare da hana shi ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Ana batun zanga zanga, Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro wani umarni

Majalisar Kano ta ƙirƙiro sababbin masarautu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar jihar Kano ta amince da ƙudirin ƙirkirar sababbin masarautu guda uku a jihar.

Ƙidirin ƙirƙirar sababbin sarakunan masu daraja ta biyu a masarautun Gaya, Karaye da Rano ya tsallake karatu na uku a majalisar a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng