Tinubu Zai Sayar da Jami’o’in Najeriya Ga Turawa? Gaskiya Ta Fito
- Ministan ilimin Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya yi karin haske kan cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta sayar da jami'o'i
- Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa akwai tsare tsare da gwamnatin tarayya ta kawo a jami'o'in Najeriya da mutane ba su fahimta ba
- Haka zalika ya yi karin haske yan yadda sababbin tsare-tsaren za su amfani Najeriya ta hanyoyin haɓaka tattalin arziki da sauransu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan jita jitar cewa za ta sayar da jami'o'in Najeriya ga turawa.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya yi karin hasken inda yace babu kamshin gaskiya cikin zancen.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya bayyana tsarin da gwamnatin ta kawo da aka yiwa mummunan fahimta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista: 'Ba maganar sayar da jami'o'i'
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta da niyyar sayar da jami'o'i.
Farfesa Tahir Mamman ya ce Bola Tinubu ta yi imani da cewa samar da makarantun gwamanti abu ne mai muhimmanci.
Tsarin da Tinubu ya kawo a jami'o'i
Farfesa Tahir Mamman ya ce an kawo tsari ne da zai ba masu zuba jari a ƙasashe daban daban damar kafa tsangayu a jami'o'in Najeriya.
Ministan ya ce wannan tsarin kuma ba sabon abu ba ne a ƙasashen da suka cigaba a ɓangaren ilimi, rahoton Tribune.
Amfanin da tsarin zai kawo ga Najeriya
Har ila yau, ministan ilimi ya bayyana cewa idan kasashe suka kafa tsangayu a jami'o'in Najeriya za a samu fa'ida sosai.
Daga cikin fa'idar da tsarin zai haifar akwai samar da kudin shiga ga Najeriya da hutar da yan kasa zuwa wasu kasashe domin karatu.
Dangote zai tallafi jami'a a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa babba mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana kudurin yin ayyuka na musamman a jami'ar jihar Kano.
Hamshakin mai kudin zai gudanar da ayyukan ne a jami'ar Aliko Dangote da ke karamar hukumar Wudil a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng