"A yi Hakuri," Sarki ya Roki 'Yan Najeriya su Ba Gwamnatin Tinubu Lokaci

"A yi Hakuri," Sarki ya Roki 'Yan Najeriya su Ba Gwamnatin Tinubu Lokaci

  • Basarake a Kudancin kasar nan ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri da mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Sarkin Legas, Oba Rilwanu Akiolu ne ya mika rokon inda ya bayar da tabbacin cewa Tinubu zai yi abin da ya dace
  • Sarkin ya kuma roki mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu ta mika kokon bararsu na bawa Legas kulawa ta musamman

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Lagos - Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Bola Tinubu domin waraka na nan zuwa. Sarkin ya yi rokon lokacin da mai dakin shugaban kasa, Remi Tinubu ta ziyarce shi a fadarsa ranar Talata.

Kara karanta wannan

Riga malam masallaci: An hango allon kamfen Bola Tinubu na zaben 2027

Remi Tinubu
Sarkin Legas ya bawa 'yan Najeriya hakuri kan mulkin Tinubu Hoto: Olusegun Adeniyi
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Oba Rilwanu Akiolu ya ce Tinubu tsayayye ne kuma za a samu canjin da ake bukata sannu a hankali.

"Tinubu na kaunar Najeriya," Sarki Oba Rilwanu

Sarkin Legas, Oba Rilwanu Akiolu ya ce shugaban kasa, Bola Tinubu na kaunar ci gaban kasar nan kuma zai yi abin da ake bukata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe cikin sanarwar dauke da sa hannun hadimar Remi Tinubu kan yada labarai, Busola Kukoyi, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri, tare da yawaita yiwa shugaban da kasa addu'a domin samun waraka a Najeriya.

"Matasa ku nemi aiki," Sarkin Legas

Sarkin Oba Rilwanu Akiolu ya roki mai dakin shugaban kasa ta mika rokonsu na bawa jihar Legas kulawa ta musamman a matsayinta na tsohuwar birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Batun gyara ake: Tinubu ya sake kora a hukumomi, ya nada sabbin shugabanni a PenCom, NSITF

Basaraken ya kuma shawarci matasan Najeriya su koyi aikin yi ba su jira sai an ba su komai ba, inda ya zarge wasu matasan da mutuwar zuciya.

Tinubu ya mika mafi karancin albashi majalisa

A baya kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai mika sabon mafi karancin albashi ga majalisa domin amsa bukatun ma'aikata.

kungiyoyin kwadago sun dade su na fafutukar tabbatar da karawa ma'aikatan kasar nan albashi, inda su ke neman N250,000 a matsayin mafi karanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.