Zargin Rub da Ciki Kan N24bn: Gwamnatin Kano Ta Maka Tsohon Kwamishina Garo a Kotu

Zargin Rub da Ciki Kan N24bn: Gwamnatin Kano Ta Maka Tsohon Kwamishina Garo a Kotu

  • Gwamnatin jihar Kano ta maka tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo a gaban babbar kotun jihar
  • Ana zargin kwamishinan Gandujen ne da yin rub da ciki tare da waddaka da N24 biliyan na kananan hukumomi
  • An shigar da kararsa ne tare da wasu kamfanoni biyu da kuma, Mustapha Sule Garo, daIsah Musa Kera

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano a ta shigar da karar tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, tare da wasu kan zargin waskar da N24bn na kananan hukumomi.

Murtala Garo ya kasance kwamishina ne har sau biyu a ma'aikatar kananan hukumomi karkashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Karshen tika tika: Kotu ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Gwamnatin Kano ta waiwayi kwamishinan Ganduje
Gwamnatin Kano ta yi karar Murtala Sule Garo, tsohon kwamishinan jiha. Hoto: Murtala Sule Garo, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Adam, mai bada shawara ga gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta yi karar mutum 6

Takardar karar da Ibrahim Adam ya wallafa ta nuna cewa, an shigar da karar mai lamba K/1330/24 gaban babbar kotun shari'a ta jihar Kano.

Kamar yadda yace, ana tuhumar wadanda ake karar da waskar da kudin al'umma wadanda aka ware domin amfanin kananan hukumomi.

Wadanda ake karar su ne: Murtala Sule Garo, Mustapha Sule Garo, Isah Musa Kera, kamfanin MJ Multipurpose Services, A.U Future Investment, da Shoreditch General Resources.

Gwamnati ta tanadin tarin shaidu

Auwal Abdulkadir Sani ne ya jagoranci gurfanarwar karkashin umarnin Antoni janar na jihar Kano.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta garzaya da takardu tare da rubutun shaidu domin shirin da tayi na zaman kotun.

Kara karanta wannan

"Muhimman cigaba 3 da za a gani bayan samun 'yanci" Inji Tsohon shugaban karamar hukuma

Takardun da ta gabatar sun hada da takardun kara, jerin shaidu da bayansu, takaitaccen bayani kan jawaban shaidu, da kuma takardun jawaban wadanda ke kara da sauran muhimman bayanai.

An maka Ganduje a Kotu

A wani rahoto na daban, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta maka Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar a gaban Kotu.

Ana zargin tsohon gwamnan jihar Kano din ne kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa da almubazzarancin Naira biliyan ashirin hudu na jihar.

An maka tsohon gwamnan a gaban kotu ne tare da tsohon Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kano, Lawan Musa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.