Emefiele: Bayan Kwace Kadarorin N12bn, Kotu Ta Hana Tsohon Gwamnan CBN Fita Waje

Emefiele: Bayan Kwace Kadarorin N12bn, Kotu Ta Hana Tsohon Gwamnan CBN Fita Waje

  • Babbar kotun tarayya dake zama a Maitama a Abuja, ta hana tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele zuwa Ingila
  • Tsohon gwamnan babban bankin ya kasa bayyana shaida dake tabbatar da cewa an gayyacesa zuwa asibiti ne kamar yadda yayi ikirari
  • Alkali Hamza Muazu ya ce Godwin Emefiele ya kasa bayyanawa kotun shaidar da tace ba za a iya maganin ciwonsa a Najeriya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya dake Maitama a Babban Birnin Tarayya, ta yi watsi da bukatar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Tsohon gwamnan na CBN ya nemi alfarmar fita zuwa Ingila ne domin duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya faɗi mafita a Najeriya

Kotu ta yanke hukunci kan bukatar da Emefiele ya gabatar
Kotu ta ki amincewa da bukatar tsohon gwamnan CBN na zuwa kasar waje. Hoto: @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

Kotu ta hana Godwin Emefiele zuwa Ingila

Mai shari'a Hamza Muazu ya ce Emefiele ya gaza kawo takardun da suka nuna cewa wannan tafiyar neman lafiyar tana da amfani wadda dole ce, jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Muazu ya gano cewa, yayin da Emefiele yayi ikirarin cewa akwai gayyata domin tafiyarsa zuwa Ingila neman lafiya, ya kasa mika kwafin gayyatar a gaban kotu.

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito, alkalin ya gano cewa, Emefiele ya ki nuna shaidar cewa ba za a iya magance ciwon da ke damunsa a Najeriya ba.

Emefiele na fuskantar tuhumar zamba

Mun ruwaito cewa an gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin a gaban Mai shari'a Muazu na babbar kotun tarayya kan zargin bayar da kwangila ba bisa doka ba.

EFCC ta zargi cewa, an bai wa Sa'adatu Ramalan Yaro, darakta a April 1616 Investment Ltd kwangiloli da yawa domin samar da motoci kirar Totota Hilux guda 45..

Kara karanta wannan

Shehin malami ya musanta karbar N16m daga Tinubu, ya fadi dalilin ziyartar shugaban kasa

Ana kuma zargin cewa matar Emefiele, Margaret da dan uwanta su ne masu kamfanin da aka ba kwangilar gyaran gidan tsohon gwamnan bankin na Ikoyi dake Legas.

Tinubu ya kori surukin Buhari daga aiki

A wani labari, mun ruwaito muku yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fatattaki Ahmed Halilu, sirikin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga wurin buga kudin Najeriya.

Lamarin ya biyo bayan samun sakamakon wani bincike da Shugaba Tinubu yasa aka yi masa a kan harkallar bankin yayin shugabancin Muhammadu Buhari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.