Cikakken Jerin Kasashe 10 da Ilmin Boko Ya Fi Yawaita a Duniya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ilmin boko na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba a cikin al'ummomin duniya, wanda hakan ya sanya ƙasashe da dama suka ɗauki ɗamarar samar da shi ga mutanensu.
Ƙasashe da dama sun shiga sahun gaba wajen samar da ilmi duba da nasarorin da suka samu a fannin.
Kasashen da ilmin boko ya yawaita
Waɗannan ƙasashen sun yi wa saura zarra wajen samar da ilmin boko mai sauƙi kuma mai inganci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shafin Bestdiplomats ya tattaro jerin ƙasashe 10 da ilmin boko ya fi yawaita a duniya a shekarar 2024.
1. Koriya ta Kudu
Koriya ta Kudu ta kasance ƙasa ta farko jerin ƙasashen da ilmin boko ya fi yawaita a duniya cikin shekarar 2024.
Ƙasar tana da kaso 97.9% na masu ilmi inda da yawa daga cikinsu sun kammala karatu a matakin gaba da sakandire.
Ƙirƙirar sababbin hanyoyin da Koriya ta Kudu ta yi a fannin ilimi, musamman a fannin fasaha da kimiyya, ya sa ta shiga sahun gaba a fannin ilimin boko a duniya.
2. Canada
Canada ita ce ƙasa ta biyu cikin jerin ƙasashe masu ilmin boko a duniya, inda ta ke da kaso 66.36% na waɗanda suka yi karatun gaba da sakandire.
Yawan jami'o'i da kwalejojin da ƙasar ta ke da su ya sanya a kodayaushe tana sahun gaba cikin ƙasashe masu yawan ƴan boko.
3. Japan
Japan ta zama ƙasa ta uku mafi ilmin boko a duniya a cikin 2024 inda take da kaso 64% na waɗanda suka kammala karatun gaba da sakandire.
Tsare-tsare da tsarin ilimi na Japan ya samar da shahararrun masu ƙirƙira a duniya.
4. Luxembourg
Ƙasar Luxemburg ita ce mafi kyawun misali wajen samun nasarar ilmin boko.
Kasar ta kasance ƙasa ta hudu a jerin ƙasashe masu ilmin boko a duniya, inda kaso 63.12% na mutanenta suka kammala karatun gaba da sakandare.
5. Ireland
Ireland tana matsayi na biyar a jerin ƙasashen da ilmin boko ya yawaita a duniya, inda take da kaso 62.88% na waɗanda suka yi karatun gaba da sakandire.
Tsarin ilimi na Ireland ya samu ci gaba na ban mamaki, tare da zuba jari mai yawa wanda hakan ya sanya ake samun ilimi mai zurfi.
Wannan nasarar ta samu ne saboda ƙarfin tattalin arziƙin Ireland, wanda ya ba da damar saka hannun jari mai yawa a harkar ilmi.
6. Ƙasar Ingila (Burtaniya)
Duba da kasancewar jami'ar Oxford, da jami'ar Cambridge, Burtaniya tana kan gaba a jerin ƙasashe masu ilimi a duniya.
Burtaniya wacce ta zo ta shida a cikin jerin, kaso 99% na mutanenta suna da ilmi, inda take da kaso 57.47% na mutanen da suka yi karatun gaba da sakandire.
7. Lithuania
Ƙasar Lithuania ta yi suna a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe masu ilimi a duniya, inda take da 57.48% na waɗanda suka kammala karatun gaba da sakandire.
8. Netherlands
Netherlands na ɗaya daga cikin ƙasashe masu ilimi a duniya, ƙasar tana da kaso 55.60% na waɗanda suka kammala karatun gaba da sakandire.
Makarantun firamare a Netherlands suna kula da yara tsakanin shekaru huɗu zuwa 12, kuma karatun sakandare wanda ya zama wajibi, ana yinsa har zuwa shekara 18.
9. Norway
Ƙasar Norway ta shahara fannin ilmi a duniya, inda kaso 100% na mutanenta ba jahilai ba ne.
Ƙasar Norway tana da kaso 55.03% na waɗanda suka kammala karatun gaba da sakandire, yayin da take ba da ilimi kyauta a kowane mataki, har zuwa jami'a domin tabbatar da cewa kowa ya samu damar samun ingantaccen ilmi.
10. Australia
Ƙasar Australia tana daga cikin jerin ƙasashen da ilmin boko ya fi yawaita a duniya.
Ƙasar tana da kaso 54% na waɗanda suka kammala karatun gaba da sakandire masu shekaru 25 zuwa 34.
Matan da ke shugabantar jami'o'i a Najeriya
A wani labarin kuma, mun kawo muku jerin matan da suka zama kallabi tsakanin rawuna inda suke shugabantar wasu jami'o'i a Najeriya.
Ta baya-bayan nan daga cikinsu ita ce Farfesa Aisha Sani Maikudi wacce ta zama shugabar riƙo ta jami'ar Abuja (UniAbuja) da ke birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng