Masu jami’o’in da ke zaman kan-su sun rugurguza ilmin Boko - Oloyode

Masu jami’o’in da ke zaman kan-su sun rugurguza ilmin Boko - Oloyode

Shugaban hukumar jarrabawar JAMB ta shiga manyan makarantun Najeriya, Farfesa Ishaq Oloyede, ya zargi shugabannin jami’o’in kasuwa da laifin taimakawa wajen tabarbarewar ilmi a Najeriya.

Farfesa Ishaq Oloyede yake cewa jami’o’in kasuwa sun bada gudumuwa na halin da harkar ilmin jami’a ya shiga a kasar nan. Shugaban na JAMB yayi wannan jawabi ne wajen wani taro na kwana 2 da aka shirya a Garin Abuja.

Oloyede yake cewa a shekarun baya ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada dama ga ‘yan kasuwa su bude jami’o’in da su taimakawa gwamnati, sai dai a cewar Farfesa Oloyede, wannan hakar da aka yi ba ba ta cin ma ruwa ba.

KU KARANTA: Yadda Gwamnati za tayi maganin zaman kashe-wando - Sarkin Kano

Shugaban jarrabawar JAMB din na kasa yace jami’o’in da ‘yan kasuwa su ka bude, su kan sabawa sharuda da dokokin da hukumar da ke kula da jami’o’i ta kafa. Hukumar NUC ta kasa ce dai ta shirya wannan zama da aka yi.

Farfesan yace duk wanda ya kai ziyara zuwa irin wadannan jami’o’i, zai san cewa babu shakka akwai matsaloli a jibge. Oloyede yace har gine-ginen kirki babu a jami’o’in. Oloyede ya daura laifin kan masu jami’o’in kasuwan kasar.

Ishaq Oloyede yace ‘yan kasuwa ne su ka kashe jami’o’in ba kowa ba, inda ya ja-kunnen makarantun da su san cewa masu rike da mukamin Vice Chancellor ne ke da hurumin tafiyar da jami’a ba wadannan masu makaranta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel