Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilimin Boko: Rochas Okorocha

Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilimin Boko: Rochas Okorocha

  • Tsohon gwamnan jihar Imo yace wajibi ne a dau hakkin ilmantar da almajirai
  • A cewarsa, wannan shine hanya daya tilo na magance matsalar tsaro
  • Rochas na daya daga cikin Sanatocin jam'iyyar APC

Abuja - Sanata mai wakiltan Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya yi kira ga masu hannu da shuni a Najeriya su taimaka wajen ilmantar da yara Almajirai ilmin zamani.

A cewarsa, idan har ana son kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, hanya mafi muhimmanci shine samar da isasshe da ingantaccen ilmi.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin karban bakuncin daliban gidauniyarsa yan kasar Sudan ta Kudu da Ethiopia a Abuja ranar Talata, rahoton Punch.

Yace jahilci na da alaka da matsalar tsaron da ake fama yanzu.

Yace:

"Wajibi dukkan masu hali a Arewaci da kudancin Najeriya su dauki akalla Almajiri daya don bashi ilmin zamani."

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan matsalar tsaron na faruwa ne saboda an sharesu, da kuma rashin adalci."
"A Najeriya muna bukatar neman Almajirai kuma mu basu ingantaccen ilmi. Da yawa daga cikinsu sun fidda rai daga zama wani abu a rayuwa."

Rochas ya kara da cewa me zai sa su fara ta'addanci idan sun fahimci cewa zasu iya zama gwamna a gobe.

A fahimtarsa, wannan shine mafita daya ga yankin Arewa.

Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilmin Boko: Rochas Okorocha
Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilmin Boko: Rochas Okorocha Hoto: PR

Asali: Legit.ng

Online view pixel