Tsuguno ba ta Kare ba: Gwamnatin Kano ta Sake Maka Shugaban APC Ganduje a Kotu

Tsuguno ba ta Kare ba: Gwamnatin Kano ta Sake Maka Shugaban APC Ganduje a Kotu

  • Gwamnatin jihar Kano ta kara maka shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje a gaban kotu
  • A wannan karon, gwamnatin na tuhumar Ganduje da hada baki da tsohon kwamishinansa wajen almubazzaranci
  • An yi zargin Ganduje da tsohon kwamishinan shari'a a jihar, Lawan Musa sun hada kai tare da wawashe N24bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Sabuwar dambarwa ta bullo a siyasar Kano bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya sake maka shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu. A sabuwar tuhumar da gwamnati ta shigar, ana zargin shugaban jam'iyyar APC da almubazzaranci da kudin talakawan Kano a zamaninsa na gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

An 'kama' wani mai kayan miya da gawarwaki da kayan makarantar yara a Kano

Abba vs Ganduje
Gwamnatin Kano ta sake shigar da Abdullahi Ganduje kara Hoto: Hon. Auwal Aranposu/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa a wannan karon, gwamnati na tuhumar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da hada baki da tsohon kwamishinan shari'a, Musa Lawan.

An zargi Ganduje da wawushe N24bn

Gwamnatin Kano na zargin Abdullahi Umar Ganduje da karya dokar kundin penal code ta jihar mai lamba 308, Jaridar Vanguard ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan jikon, gwamnatin na zargin Ganduje ya hada baki da tsohon kwamishinansa wajen mayar da N24bn na jama'ar Kano aljihunsu.

"Mun tanadi shaidu," Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje gaban kotu.

Ta ce ta tanadi shaidunta guda hudu da za su tabbatar wa kotu zargin da su ke yi na wawashe kudin jama'a da Ganduje ya yi.

Har yanzu kotu ba ta sanya ranar fara sauraron shari'ar da aka shigar ba, yayin da ake wata shari'a kan zargin Ganduje da mai dakinsa da wasu mutum shida da zamba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, ya faɗi mafita a Najeriya

Kotu ta fusata da halin Ganduje

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta fusata da yadda Abdullahi Ganduje da matarsa ke kin martaba umarninta.

Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta bayar da umarnin a cafko tsohon gwamnan domin ya bayyana a gabanta kan karar da gwamnatin Kano ta shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.