An 'Kama' Wani Mai Kayan Miya da Gawarwaki da Kayan Makarantar Yara a Kano

An 'Kama' Wani Mai Kayan Miya da Gawarwaki da Kayan Makarantar Yara a Kano

  • Jama'ar Dawakin Kudu sun shiga dimuwa bayan an kama wani mai kayan miya Abdul-Aziz da gawarwakin mutane kulle a gidansa
  • Daga cikin gawarwakin akwai ta amininsa da ake zargin rufe a cikin ramin shadda da ta tsohon mai gidansa da aka sace a shekarun baya
  • Haka kuma an gano rigunan 'yan makaranta da ake zargin mai kayan miyan ya kashe yaran ne ko ya sauya masu wuri

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jama'ar karamar hukumar Dawakin Kudu sun shiga tashin hankali bayan an gano gawarwaki a gidan wani mai sayar da kayan miya, Abdul-Aziz. An samu mabanbantan ra'ayoyi kan adadin gawarwakin da aka gano, inda Al'amin Ibrahim ya ce ana tunanin sun kai shida ne kamar yadda ya gani.

Kara karanta wannan

A karo na 2, gwamnatin Abba gida gida ta fara rabon tallafin kudi ga mata 5,200

Jihar Kano
An gano gawarwaki a gidan mai sayar da kayan miya Hoto: Tijjani Adamu
Asali: UGC

A hirar Legit da wata Adama Sallau wacce aka sace mata 'yan uwa gida biyu, ta ce Abdul-Aziz ya fi kowa arhar kayan miya a yankin.

Yadda aka gano gawarwakin

Adama Sallau ta ce Abdul-Aziz ya shiga hannun jami'an tsaro bisa zargin garkuwa da mutane. Matar ta ce kusan sati guda kenan da kama shi, sai matasan da ke kwana a jikin gidansa su ka ji wari na tasowa daga cikin gidan uban gidan Abdul-Aziz. Haka ta sa matasan su ka haura gidan, kuma aka gano gawar tsohon mai gidan Abdul-Aziz a kan gadonsa ya na zagwanye wa. Ta ce ana zargin Mai kayan miyan ya na ƙamar da gawar tsohon mai gidansa, Ali Nagana da hoda, amma bayan an kama shi sai gawar ta fara wari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adama Sallau na neman yan uwanta 2

Cikin bacin rai da fusata Adama Sallau ta ce ana zargin Abdul-Aziz ne ya sace dukkanin wadanda ake sacewa a Dawakin Kudu da kewaye. Ta ce akwai yan uwanta guda biyu da a yanzu haka ake tunanin Abdul-Aziz ya sace. Adama Sallau ta bayyana yadda aka sace mutane biyu daga danginta;

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: An harbi tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a wani taro a Pennsylvania

1. Abba mai shekaru 30

Adama ta bayyana cewa an sace dan uwan yaranta, magidanci mai shekaru 30 da ake kira Abba.

Ta ce a waya kawai aka yiwa Abba, ana neman a hadu da shi a wani waje. Kuma ya je sai aka dauke shi a mota.

Adama ta ce an hakikance Abdul-Aziz mai kayan miya ne ya dauke shi, amma ba a ga gawarsa a cikin gidan ba, saboda haka ba a san halin da ake ciki ba.

Matar ta shaidawa Legit cewa har an fara biyan wani kaso na kudin fansar da aka nema.

2. Matashi mai shekara 20

Duk da ba ta bayyana sunansa ba, Adama ta ce yanzu zargin Mai kayan miya da sace wani dan uwanta mai shekaru 20 wanda ke da tabin hankali.

Ta ce matashin ba ya duka ba ya zagi kuma ya san kowa a Dawakin Kudu, kowa ya san shi.

Kara karanta wannan

Rijiyar Kolmani: Gwamnan Arewa ya gana da Tinubu kan batun hako mai a Arewa

Gawarwaki nawa aka gano?

Al'amin Ibrahim, mazaunin Dawakin Kudu da lamarin debo gawarwakin ya wakana a gaban idonsa ya shaidawa Legit cewa an gano kasusuwan jama'a.

Baya ga kasusuwa da wasu sassan dan Adam da su ka rube, an gano gawarwakin mutum biyu.

Adama ta ce gawar aminin mai kayan miya Kolo da aka sace kwanaki 14 da su ka wuce a gidan AbdulAziz, sai ta mai gidansa a gidan marigayin kwance kan shimfida

Me aka kara ganowa a gidan Abdul-Aziz?

Daga cikin abubuwan da Adama da Al'amin su ka ganewa idanunsu an gani a gidan mai kayan miya akwai Farar kaza.

An kuma gano kayan makarantar yara da wasu abubuwa masu kama da kayan tsafi.

Abdul-Aziz gardi ne da ya sauka a garin Dawakin Kudu shekaru 12 da su ka gabata.

An ceto 'yar shekara 2 a Kano

A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta samu nasarar ceto wata yarinya mai shekaru biyu bayan an yi garkuwa da ita.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame gidan wani da ake zargi da alaƙa da ƴan bindiga

An gano yarinyar bayan cafke makocinsu da ya sace ta, sannan ya kai ta makota inda ya boye yarinyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.