"Kotu ta yi Adalci," Gwamnatin Abba ta Jinjina Hukuncin Rikicin Masarautun Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin kotu kan dambarwar masarautar Kano ba abin mamaki ba ne
- Hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a yau Talata
- Ya ce Kanawa su na zaune cikin kwanciyar hankali domin dama hukuncin da su ke so a zartar ke nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta ce ba ta yi mamakin hukuncin kotu da ya tabbatar da nadin Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ba.
Kotu ta haramta wa sarki Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan masarautun Kano hudu daga bayyana kansu da sarakai.
A wata hira da daraktan janar kan yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi da Arise TV, ya ce kotu ta yi adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kanawa sun ji dadin hukuncin kotu," Sanusi
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa jama'ar Kano na zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ɗar-ɗar ba.
Sanusi Bature, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnan Kano ya ce hukuncin kotu ya yi wa mazauna jihar dadi.
Ya ce abin da kotu ta yi shi ne tabbatar da dokar kasa da ta ba gwamna Abba Kabir Yusuf damar sauke sarakuna da nada sabo.
"Lokacin mutunta hukuncin kotu ya yi," NNPP
Jam'iyyar NNPP reshen Kano ta ce lokaci ya yi da tuɓaɓɓun sarakunan masarautun jihar biyar za su yi biyayya ga umarnin kotu.
Kakakin jam'iyyar, Musa Nuhu 'Yankaba ya shaida wa Legit cewa yanzu ya kamata sarakunan su bar masarautun.
Ya ce lokaci ya yi da sarki Sanusi II zai nada hakimai a fara mulkin sarauta a Kano, inda ya yaba da hukuncin kotun.
Rikicin sarauta: Kotu ta yi hukunci
A baya mun ruwaito cewa babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar jihar.
A hukuncin da ta zartar, Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta haramta wa sarakunan masarautun jihar biyar su dai na bayyana kansu da sarakai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng