Sanusi II vs Aminu Ado: An Caccaki Abba Kabir da Kwankwaso Kan Hukuncin Kotu

Sanusi II vs Aminu Ado: An Caccaki Abba Kabir da Kwankwaso Kan Hukuncin Kotu

  • Yayin da aka yanke hukunci kan dambarwar sarautar Kano, kungiya ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso
  • Kungiyar mai suna Kano Democratic Vanguard ta ce hukuncin abin kunya ne ga bangaren shari'a duba da yadda aka nuna son kai karara
  • Hakan ya biyo bayan hukuncin kotu inda ta dakatar da sarakunan guda biyar da aka tube kan ci gaba da kiran kansu sarakai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Kano Democrat Vanguard ta yi martani bayan hukuncin kotu game da sarautar Kano.

Kungiyar ta caccaki Gwamna Abba Kabir da zargin nuna son kai da saba doka a hukuncin da kotu ta yi.

Kara karanta wannan

Babbar Kotu ta bada sabon umarni ga Aminu Ado Bayero da sauran Sarakunan da aka tsige

Kungiya ta soki Abba Kabir kan rigimar sarauta tsakanin Sanusi II da Aminu Ado
Kungiya a Kano ta yi martani bayan hukuncin kotu game da dambarwa tsakanin Aminu Ado da Sanusi II. Hoto: @Kyusufabba, @HrHBayero.
Asali: Twitter

Kano: Kungiya ta yi fatali da hukunci

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Legit ta samu a jiya Litinin 15 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta yi Allah wadai da hukuncin inda ta ce akwai tsantsar son kai da kuma saba ka'idar doka.

Wannan na zuwa ne bayan hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu daga ci gaba da kiran kansu sarakai a jihar.

Sarautar Kano: Kungiya ta soki Abba, Kwankwaso

Kungiyar ta caccaki Gwamna Abba Kabir da Rabiu Kwankwaso wurin rusa masarautun domin biyan buƙatar kansu, cewar The Nation.

Ta ce Abba da Kwankwaso sun mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar Kano duk da sun sani ƴan jihar ba su goyon bayan haka.

"Gwamna Abba Kabir da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso sun sake cin mutuncin bangaren shari'a game da sarautar Kano."

Kara karanta wannan

Karshen tika tika: Kotu ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano

"Sun rusa masarautun da suka dade shekara da shekaru da kuma tuge Aminu Ado yayin da suka mayar da Sanusi II duk da jama'a ba su son dawowarsa."
"Hukuncin ya kara tabbatar da neman ikonsu da kwadayin mulki a fili, muna kira ga jama'ar Kano da su kwantar da hankalinsu gaskiya za ta yi halinta."

- Democratic Vanguard

Kwankwaso ya fadi dalilin cire Aminu Ado

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana dalilin Gwamna Abba Kabir na cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Kwankwaso ya ce Abba ya dauki matakin ne domin cika alkawuran da ya dauka tun lokacin kamfe ga al'ummar jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.