Karshen Tika Tika: Kotu ta Yanke Hukunci kan Dambarwar Masarautar Kano

Karshen Tika Tika: Kotu ta Yanke Hukunci kan Dambarwar Masarautar Kano

  • A yau Litinin babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta kawo karshen rikicin masarautar jihar bayan ta yanke hukunci
  • Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta shigar da kara ta na neman a haramtawa Aminu Ado Bayero kiran kansa sarki
  • A hukuncin da ta zartar, Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta haramta wa Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran tubabbun mutum hudu kiran kansu sarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta kawo karshen rikicin masarautar Kano, inda ta yanke hukunci a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Zargin N33bn: Bayan kwana 1 a kurkuku, kotu ta ɗauki mataki kan Ministan Buhari

Kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta haramta wa Aminu Ado Bayero da bayyana kansa a matsayin sarki.

Kotu Kano
Kotu ta yanke hukunci kan rikicin masarautar Kano Hoto: Muhammad Sanusi II/Masarautar Kano
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Alkaliyar ta haramta wa sarki Bayero da sauran sarakunan masarautun Bichi, Rano, Gaya da Karaye a da kiran kansu sarakuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da bukatar gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta yi nasara a kotu bayan da aka tabbatar da rokonta na hana sarki Aminu Ado Bayero da bayyana kansa a matsayin sarki, Justice Watch News ta wallafa.

Wannan na zuwa ne bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya ki amincewa da tube rawaninsa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.

A hukuncin da ta zartar yau Litinin, Alkaliyar babbar kotun jiha ta hana Bayero da sauran wadanda aka sauke daga bayyana kansu a matsayin sarakunan jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta yi fatali da bukatar 'Chuchu' da ake zargi da kisan Nafi'u

Kotu ta dauki mataki kan tsige sarki

A baya mun ruwaito cewa babbar kotun jiha da ke sauraren shari'ar dambarwar masarautar Kano ta dauki matakin kan rikicin inda ta dage zama.

Mai Shari'a Aminu Adamu Aliyu ta dage ci gaba da sauraron karar da gwamnatin Kano ta shigar ta na kalubalantar Aminu Ado Bayero da ke ci gaba da kiran kansa sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.