Ta Leko Ta Koma: Tinubu Ya Tsige Adekanmbi Kwanaki 2 da Nada Shi Shugaban HYPREP
- Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana korar Olufemi Adekanmbi a matsayin shugaban gudanarwa na shirin HYPREP
- Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da nada shi shugaban hukumar, ya maye gurbinsa da tsohon shugaban da aka tube
- Kamar yadda aka gano, an yi bitar kwazon Farfesa Nenibarini Zabbey, lamarin da yasa aka ce ya dace ya cigaba da shugabantar hukumar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire Olufemi Adekanmbi daga matsayin shugaban na shirin magance matsalar gurbacewar iska na HYPREP.
Wannan na zuwa ne bayan sa'o'i 48 bayan yi masa nadin. A hukumance an nada Adekanmbi wannan matsayin shugaban HYPREP ne a ranar Asabar.
HYPREP: Tinubu ya dawo da Farfesa Zabbey
A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya sanar da cewa Tinubu ya mayar da Farfesa Nenibarini Zabbey a matsayin shugaban HYPREP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Ngelale ya ce, wannan hukuncin ya biyo bayan bitar kwazon Fafesa Zabbey da Shugaba Tinubu yayi inda aka gano ya cancanci ya cigaba da rike matsayin.
Sanarwar ta ce:
"Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da mayar da Farfesa Nenibarini Zabbey bakin aiki a matsayin shugaban shirin magance gurbacewar muhalli na (HYPREP)."
Buhari ne ya fara nada Zabbey a HYPREP
Sake dawo da Farfesa Zabbey ya fara aiki ne a nan take, kamar yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayi umarni.
Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara nada Farfesa Zabbey a matsayin shugaban hukumar a watan Mayun 2023 bayan wa'adin Giadom Dumbari ya kare.
Duba sanarwar da Daddy Olusegun, mai tallafawa Shugaba Tinubu ta fuskar kafofin sada zumunta ya wallafa a shafinsa na X.
Tinubu ya kirkiro sabuwar ma'aikata
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kirkiro sabuwar ma'aikata a matakin tarayya.
Ya kirkiro ma'aikatar kiwon dabbobi da ake sa ran za ta magance matsalar manoma da makiyaya da ta ki ci balle cinyewa a fadin Najeriya.
An tabbatar da kirkiro sabuwa ma'aikatar ne yayin wani taron kaddamar kwamitin aiwatar da gyara a fannin kiwon dabbobi wanda aka yi a fadar shugaban kasan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng