"Muhimman Cigaba 3 da Za a Gani Bayan Samun 'Yanci" Inji Tsohon Shugaban Karamar Hukuma

"Muhimman Cigaba 3 da Za a Gani Bayan Samun 'Yanci" Inji Tsohon Shugaban Karamar Hukuma

  • Kusoshin kasar nan da masu ruwa da tsaki a harkar tafiyar da kananan hukumomi na ci gaba da fadan alfanun ba Ciyamomi 'yanci
  • Tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo a Kano, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya ce yanzu jama'a za su mori zaben da su ke yi
  • Injiniya Ramat ya shaidawa Legit cewa matukar za a ba kananan hukumomi dama kamar yadda kotu ta tabbatar, za a zamu karuwar arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya ce lokaci ya yi da jama’a tun daga tushe za su mori dimukuradiyya.

Kara karanta wannan

Rijiyar Kolmani: Gwamnan Arewa ya gana da Tinubu kan batun hako mai a Arewa

A tattaunarsa da Legit, tsohon shugaban karamar hukumar a gwamnatin Abdullahi Ganduje ya ce samun ‘yancin gashin kai da kotu ta tabbatarwa kananan hukumomi abin murna ne.

Engr Abdullahi Garba Ramat
Tsohon shugaba ya fadi alfanun bawa kananan hukumomi 'yancinsu Hoto: Engr Abdullahi Garba Ramat
Asali: Facebook

Ya ce nan gaba kadan, matukar hukumomi irin su ICPC da EFCC da sauran masu ruwa da tsaki su ka tabbata an bar kananan hukumomin su na gudanar da lamuransu, za a samu alkhairi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za a fara manyan ayyuka," Ramat

Tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Injiniya Abdullahi Garba Ramat ya bayyana cewa saura kiris gwamnonin jihohi su fara neman ayyukan yi su na rasa wa.

A hirarsa da Legit, ya ce akwai manyan ayyuka da kanana da su ke alhakin karamar hukuma ce ta yiwa jama'ar da su ka zabe ta.

Ya lissafa wasu manyan ayyuka uku da cin gashin kan kananan hukumomi zai samar ga mutanen karkara;

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi: Tsohon gwamna ya soki hukuncin kotu, ya fadi illar haka ga Najeriya

1. Inganta harkar lafiya

Injiniya Ramat ya ce 'yancin kananan hukumomi zai kawo gyaruwar asibitocin da ke karkara, wanda hakan zai inganta lafiya.

Tsohon shugaban karamar hukumar ya ce daga ayyukan ya rataya a wuyansu akwai inganta lafiya da gina asibitoci.

2. Rage Talauci tsakanin jama'a

Injiniya Abdullahi Ramat na ganin yayin da gwamnoni ke wasu ayyuka da a zahiri su ke na kananan hukumomi, tabbatar da 'yancinsu zai habaka sana'o'i.

Tsohon shugaban na ganin ayyukan kananan hukumomi ne tallafa wa masu kananan sana'o'i wanda yanzu gwamnatocin jiha ke yi.

Ramat ya ce matukar da gaske za a saki kananan hukumomi su juya akalar yankunansu, nan gaba kadan za a kakkabe talauci tsakanin mutanen karkara.

3. Kawar da rashin tsaro

Gudanar da ayyukan ci gaban kasa a kananan hukumomi zai taimaka wajen rage matsalar tsaro koma kawar da shi gaba daya, inji Injiniya Ramat.

Kara karanta wannan

Zargin N33bn: Bayan kwana 1 a kurkuku, kotu ta ɗauki mataki kan Ministan Buhari

Ramat, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo ne ya ce matukar da gaske ake za a tabbatar wa da kananan hukumomi 'yancin su kamar yadda kotu ta ce, za a rage matsalar tsaro.

"Ba nasara a yancin kananan hukumomi," Fayose

A wani labarin kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa duk da hukuncin kotu, kananan hukumomi ba za su samu 'yanci ba.

Ya ce kotun ba za ta iya raba jihohi da kananan hukumominsu ba, saboda haka majalisun dokoki na jihohi da gwamnoni za su ci gaba da takura masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.