Yadda Sheikh Jafar da Wasu Malamai Suka Jagoranci Zanga Zanga a Kano a 2003

Yadda Sheikh Jafar da Wasu Malamai Suka Jagoranci Zanga Zanga a Kano a 2003

  • Malaman addinin Musulunci a Arewacin Najeriya na cigaba da bayani kan zanga zanga da ake kokarin gudanarwa a fadin kasar
  • Farfesa Salisu Shehu ya tuna baya yadda suka jagoranci zanga zanga tare da su Sheikh Jafar Mahmud Adam a jihar Kano
  • Malamin addini da bokon ya bayyana yadda zanga zangar ta kasance da abubuwan da suka biyo bayanta a wancan lokacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Malaman addinin Musulunci na cigaba da jan hankulan al'umma kan gudanar da zanga zanga.

Shugaban jami'ar Al-Istiqamah da ke Sumaila a jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu ya bayyana yadda suka yi zanga zanga a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun nuna turjiya bayan an yi musu ruwan borkonon tsohuwa

Salisu Shehu
Yadda malamai suka yi zanga zanga a 2003. Hoto: Professor Salisu Shehu
Asali: Facebook

Farfesa Salisu Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa cikin malaman da suka jagoranci zanga zanga a 2003 har da Sheikh Jafar Mahmud Adam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin yin zanga zangar Kano a 2003

Farfesa Salisu Shehu ya bayyana cewa sun fita zanga zanga ne domin nuna kin amincewa da mamayar da Amurka ta yi a Iraqi.

Malamin ya ce a shekarar 2003 abin ya faru kuma hakan ya jawo zanga zanga a kasashen Musulmi a fadin duniya.

Malaman da suka fita zanga zanga lokacin

Farfesa Salisu Shehu ya bayyana cewa Sheikh Jafar, Sheikh Isa Waziri, Sheikh Ibrahim Kalil na cikin malaman da suka fita zanga zanga tare.

Ya ce sun fita daga masallaci suka bi ta State Road har gidan gwamnati suka mika takarda domin kai wa ga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun fandare, sun nufi gidajen manyan Najeriya a Abuja

Abin da ya biyo bayan zanga zangar

Har ila yau Farfesa Salisu Shehu bayyana cewa bayan sun watse kawai sai yara suka shiga gari suna barna da sunan zanga zanga.

Malamin ya ce matasa sun yi barna sosai ciki har da asarar dukiya da rayuka kafin a shawo kansu da kyar.

Saboda haka ne Farfesa Salisu Shehu ya ce suke kin zanga zanga domin kaucewa rikicin da zai biyo baya musamman a yanzu da bata gari suka kara yawa a cikin al'umma.

Zanga zanga: Ana kokarin ganin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tattaunawa a kafafen sada zumunta kan shirin fita zanga zanga na cigaba da ɗaukan hankalin al'ummar Najeriya.

A yanzu haka wasu daga cikin malamai sun fara yunkurin ganin an gana da shugaban kasa kan magance matsalolin tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng